Kuna tsoron yin magana?

Kada kuji tsoro. Kun cancanta a saurare ku

Yin magana zai iya tsorota wasun mu.

Muna tsoro kada a hukunta mu ko kuwa ayi mana azaba.

Kuma muna damuwa cewa mai yiwuwa mu bata wa iyayen mu rai ko kuwa abokan mu da abun da zamu fadi.

Wannan ne ya saka wasu lokuta muke tunanin yin shiru zai fi kawai. Shiyasa idan wani abu mara kyau ya faru muna shiru.

Amma gaskiyar shine wasu lokuta yana da muhimmanci kuyi magana musamman idan ana raunata ku ko kuwa ana kankanta ku.

Zai iya kawo sauki.

Yin magana zai iya taimakon ku kare kanku. Idan kuka gaya wa mutane yadda suka saka ku ji zasu iya koya daina maimaitawa.

Kuma zai iya saka ku kare mutane dake kusa daku. Ga misali, idan kuka yi magana zaku iya taimakon wani makwaftar ku ko abokiya da ake cin zali. Idan kuna tsoron fuskance masu cin zalin, zaku iya kai rahoton su zuwa wani babban mutum.

Amma yin magana baya nufi cewa kuyi ihu ko rashin ladabi.

Yana nufin cewa zaku yi magana da da’a amma kuma da tabbaci. Ga misali, maimakon kuyi ihu ko ku zage abokan ku domin sun bata muku rai. Zaku iya fadi da hankali cewa “Nayi bakin ciki da abun da kika yi, ban taba tsammanin zaki iya yin wannan abun ba”

Ko kuwa idan kuka ga ana cin zalin wata, zaku iya yin musu magana da hankali kuce *“Ina bukatan ku ku daina abun da kuke yi ko na kai rahoton ku a wajan wani babba”. Wannan yafi yin fada. Baku da wani dalilin jin tsoro. Kada ku bari wani ya tsorata ku yin shiru.

Muryan ku ne. Kuyi amfani dashi ma abu mai kyau ku kare wadanda basu da bakin yin magana.

Zaku iya samun girmamawa daga wajan sauran mutane kamar yarinya dake fadin ran ta. Ku tuna kuyi magana da girmamawa.

Wasu lokuta idan kuka yi magana mai yiwuwa mutane baza su maida martani a yadda kuke tsammani ba. Idan wannan ya faru, zai iya kashe muku jiki. Yana da muhimmanci idan baku bari wannan ya hana ku ba. Idan kuka yi magana, zaku kara gina tabbacin ku da kuma aunin darajar ku. Kuma wadannan halayen nada muhimmanci a rayuwar ku.

Kuna ji kamar akwai wajaje da baza ku iya magana ba? Kuna jin tsoron gaya wa mutane yadda kuke ji? Kuyi mana magana a sahin sharhi.

Share your feedback