Nuna shauki bai zuwa da sauki

Ku fadi abun dake ran ku yan mata!

Idan wani zai baku miliyan daya yanzu nan, ya zaku ji? Zaku yi farin ciki?

Mun san cewa abun da zaku yi shine raba wannan labarin mai dadi da wani dake kusa daku.

Yanzu, a haka kuke nuna shaukin ku.

Saboda haka kun ga cewa nuna shauki abun al’ada ce.

Eh, mun san cewa ba kowane shauki bane zamu iya rarrabawa. Ga misala, nuna wa wani babba wai kuna fushi dasu ko kuwa gaya wa wani da kuke sha’awa wai kuna son sa. Mai yiwuwa ma kuji tsoron yadda zasu amsa ku.

Kuma wasu lokuta, wasun mu na boye yadda muke ji domin bamu so a kira mu masu rauni.

Mai yiwuwa kunji abubuwa kamar “Manyan yan basu kuka, ko kuwa kuka na kananan yara ne”? Toh, duk wannan karya ne.

Ku mutane ne kuma kuna da wani abu da ake kira shauki.

Shauki bayanai ne akan yadda kuke ji akan wani ko wani abu. Ga misali, fushi, farin ciki, bakin ciki, da sauran su. Nuna wadannan hallayan baya nufi cewa ku masu rauni ne. Yana nufin cewa kuna da karfi kuma kun gane kanku kuma baku tsoron nuna yadda kuke ji.

Kuma idan kuka bayyana wannan, zaku kara jin farin ciki.

Idan kuka nuna yadda kuke ji mutane dake kusa daku zasu fahimce ku da kyau. Zai taimake su gane yadda zasu aikata wasu halayye a kusa daku.

Ga misali, ace wata abokiyar ku tace wani abu daya saka ku bakin ciki kuma kuka yanke shawara ku boye yadda kuke ji. Kun san abun da zai faru?

Saboda kun yanke shawara ku boye yadda kuke ji, mai yiwuwa abokan ku baza su san cewa sun bata muku rai ba. Kuma mai yiwuwa su maimaita wannan halin da zai sake bata muku rai.

Amma idan kuka nuna musu cewa kalmomin su ya saka ku bakin ciki, mai yiwuwa su baku hakuri kuma baza su sake maimaita shi ba.

Toh zaku fi son kuyi shiru ko kuwa kuyi magana kuma hankalin ya kwanta?

Rike abu a zuciya bashi da kyau. Zai iya jawo tashin hankali ko kuwa bakin ciki.

Saboda haka yan mata, kuna bukatan yin magana. Babu tsoro. Idan kuna jin tsoron nuna yadda kuke ji fuska da fuska, zaku iya tura sakon rubutu, wasika, ko kuwa ku kira mutumin a waya.

Idan mutumin ya girme ku, zaku iya tambayan wani amintaccen babba ya taimake ku yin musu magana.

Kuje ku bayyana kanku yau.

Kuna kasa nuna yadda kuke Ji? Meyasa? Kuyi mana magana a sashin sharhi.

Share your feedback