Yin magana zai iya cecin ki

Yadda zaki fara tattaunawa da iyayen ki ko kuwa dan dangin ku daya girme ku

“Iyaye na baza su gane ba”

Dukkan mu mun taba fadin wadannan kalmomin.

Gaskiyar shine muna bukatan koyan yadda zamu yi wa iyayen mu ko dangin daya girme mu magana. Saboda su fahimce mu da kyau. Mun san cewa yin wa iyayen mu magana zai iya tsorata mu.

Idan baku yin wa iyayen ku magana kowane rana, zai iya yin wuya ku yi musu maganan daya dace. Saboda haka ku fara musa magana akan yan kankanin abubuwa. Zaku iya tambayan su yadda ranan su yake ko kuwa kuyi musu magana akan naku ranan.

Ga wasu sidabbaru da zai taimaka mana sauki.

Ku samu dabara.

Kafan kuyi wa iyayen ku magana kuna bukatan yin wadannan abubuwan;

  1. Kuyi tunanin abun da kuke son ku fada.
  2. Rubuta su.
  3. Zabi abun da kuke son kuyi magana akai- kuna son kuyi magana da daya daga cikin iyayen ku ne ko kuwa su biyun su tare? Ko kuwa kuna son daya daga cikin iyayen ku ya taimaka yayi wa dayan magana.
  4. Kuma kuna bukatan setin lokacin- shirya maganganun ku a lokacin da iyayen ku basu da aikin yi sosai saboda su mayar da hankali a kan ku.

Ku zama jarumai

Kada ku yarda damuwa akan abun da iyayen ku zasu iya fadi ya hana ku yin musu magana. Koda menene darasin, idan kuka yi magana akan sa da iyayen ku, damuwan zai tafi.

Ku zama bayyanannu da kuma kai tsaye

Idan kuka yi magana da iyayen ku kuna bukatan natsuwa saboda su fahimce ku da kyau. Banda karin gishiri. Ku fadi gaskiya. Kuyi da sauki kuma sarai. Su san abun da kike tunani, abun da kike ji da kuma abun da kike so. Yana da muhimmanci iyayen ki su fahimce komai da kike fadi.

Saurara

Abun muhimmanci akan sadarwa shine ikon yin shiru kuma a saurarawa. Ku tabata kun gane abun da iyayen ku ke fadin muku saboda mu mayar da martani da kyau. Idan baku yarda da abun da suke fadi ba, Kuyi musu magana da mutunci. Idan kuka yi haka zasu dauke abun da kuke fadi da tsanani.

Kuna da wani sidabbaru na yin wa iyaye magana? Gaya mana!

Share your feedback