Ku rike ra’ayin ku da karfi da kyau

Ku mallake ra’ayin ku da alfahari

Tunanin ku (4)

Kuna da karfi fiye da kuke tunani. Akwai wani karfi na musamman a cikin ku. Yana baku karfin halin fadin ran ku akan kowane abu. Yadda kuke son duniya ya kasance, da muradin ku, da sauran su.

Amma akwai mutanen da baza su yadda da ra’ayin ku ba. Musamman idan ra’ayin ku ya bambanta da nasu. Wasu mutane na tunanin cewa bai kamata mata su sami ra’ayi da muradi ba. Suna tunanin cewa yakamata yan mata su zauna suyi shiru. Wadannan mutanen zasu so su canza muku ra’ayi. Mai yiwuwa ma su gaya muku wasu kalmomi masu raunata. Ko kuwa su so su hanna ku fadin ran ku da cimma burin ku.

A lokuta kamar haka, ku rike ra’ayin ku da karfi kuma ku mallake su. Kada ku janye baya domin ku gamsar da wani. Ko kuwa ku canza ran ku don kuna son mutane su yabe ku. Dukkan mu na ganin abubuwa daban-daban. Shiyasa bamu yarda da ra’ayin juna wasu lokuta.

Eh, yana da muhimmanci ku samu naku ra’ayin. Amma zai iya yin wuya idan ku kadai ne a al’ummar ku da wadannan ra’ayin. Duk da haka, abun da yasa kuka kasance masu musamman kenan. Ku cikakken mutane ne da naku ra’ayin.
<br Saboda haka a nan gaba idan wani yana son ya canza muku ra’ayi, ku ja dogon nunfashi, sai ku kirga daga daya zuwa goma a zuciyar ku. Bayan nan, ku maimaita ra’ayin ku da hankali. Kada kuyi ihu. Idan kuna ji kamar kuna cikin wani matsala, ku bar wajan nan take. Ku kai rahoton mutumin a wajan wani amintaccen babban mutum.

Ku tuna, muryan ku ne makamin ku mafi karfi. Mallakin ku ne. Kada wani ya gaya muku wani abu daban. Idan kuna son ku zama farkon mace mai buga kwallo a al’ummar ku, kuyi sa. Eh zaku iya yi, kuma zaku yi, yan mata! Kada ku saurarre wadannan da zasu ce bazai iya yiwuwa ba. A maimako, ku mai da hankali a cimma muradin ku. Kuyi aiki sosai domin kuci nasara. Zaku iya farawa ta yin gwaji kowane rana. Ko kuwa yin magana da wani dake imani daku. Kada ku fid da rai; zai biya a karshe.

Kun taba daukan wani matsayi wa wani abu da kuke imani da? Me kuka ce? Ya ya kasance? Tambayoyi da yawa. Muyi magana a sashin sharhi.

Share your feedback

Tunanin ku

LLLOIL

March 20, 2022, 7:57 p.m.

Latest Reply

inason aure

aikina keso

March 20, 2022, 7:57 p.m.

wasulokuta dasuka wuce nageria bA stari

March 20, 2022, 7:57 p.m.