Ku daina yin uzuri, ku kai rahoto

Yakamata a bi daku da mutunci

Kun cancanta a bi daku da hankali. Kuma al’ada ce ku tambaya abunda kuke cancanta. Kuma ba komai idan kuka amince cewa kuna son a bi daku fiye da yadda ake bi daku yanzu.

Duk da kuke son a bi daku da hankali, wasu mutane ba zasu yi ba. Wasu lokuta zasu yi abubuwa da zai saka ku bakin ciki.

Kamar wani tsohon makwafci ya riga muku fito duk sanda kuke wucewa. Ko kuwa ya gwada taba ku.

Ko kuwa wata babban yarinya a ungwan ku ta riga tsokanan ku. Mai yiwuwa ta riga zagin ku. Mai yiwuwa ma tana dariyar kayan da kuke sakawa.

Zai iya zama wani daga cikin yan iyalan ku da zai riga fadin muku abubuwa mara kyau. Mai yiwuwa suna zagin ku ne. Ko kuwa su saka ku ji kamar rayuwar ku ba zai kasance da kyau ba.

Ba laifin ku bane idan suna aikata halayyar nan.

Shiyasa bai kamata ku riga musu uzuri ba. Ya kamata kuyi magana.

Idan baku yi ba, halayyar su zai shafe aunin girman ku da tabbacin ku. Zai iya saka ku bakin ciki.

Idan kuka cigaba da yin shiru zasu kara raunata ku. Kuma gaskiyar shine mai yiwuwa su ci nasara.

Idan ba’a kula ba zaku fara bawa kanku laifin yadda suke bi da ku. Mai yiwuwa ma ku fara yin musu uzuri. Yawancin lokuta tsoro ne ke jawo wannan.

Tsoron cewa mai yiwuwa zasu raunata ku idan kuka yi magana.

Eh mai yiwuwa kuyi tsoron yin musu magana fuska da fuska. Amma bai kamata kai rahoton su ya tsorata su ba.

Ku kai tahoton wannan tsohon makwafcin nan zuwa wajan wani amintaccen babban mutum yau. Wannan mutumin da kuka san cewa bai zai hukunta ku ba ko kuwa ya saka ku jin wani iri idan kuka yi musu magana. Zai iya zama wani da kuka yarda da.

Ku tuna ba sai kunyi sa da fitina ba. Baku bukatan zagin su kuma kada ku sake ku gwada shawo kan matsalar da tashin hankali.

Koda menene ko kuwa kowaye ne, ku kai rahoto, kuyi wa wani magana akan yadda kuke ji, ku naima taimakon mutane su goya muku baya. Farin cikin ku da kwanciyar hankalin ku nada muhimmanci.

Kun taba jin tsoron kai rahoton wani? Gaya mana abun da kuke yi a karshe a sashin sharhi.

Share your feedback