Yin amfani da shafin yanar gizo gizo nada sauki kamar ABC

Duniya a yatsun hanun ku

Mun yi sa’a an kirkira yanar gizo gizo! A da, mutane na neman takarda ko kuwa su tambaye wani duk lokacin da basu san akan abu ba. Yanzu, zamu iya neman abubuwa da yawa akan yanar gizo gizo. Muyi magana game da wasu kayan aikin yanar gizo gizo da muka fi so.

Mabincikar bayanai

Wannan yana barin ku samun damar amfani da yanar gizo gizo da kuma shafukka dake da masaukin bayanai da kuke naima. Ku nemo su a jerin mazabar wayar ku. Idan mabincikar bayanai da yazo da wayan ku bai da sauri, ku saukar da wani mabincikar bayanai mai sauri kamar Google Chrome ko kuwa Opera Mini zuwa wayar ku. Da zaran kuka samu daman shigan yanar gizo gizo zaku iya yin abubuwa da yawa. kamar naiman bayanai na aikin makaranta, ko ku kallon wani bidiyo domin ku koya wani sabon kwarewa, kuma zaku iya samun sabobin labarai.

Bincika

Wannan ne sirrin neman amsa a yanar gizo gizo. Ku nema wani akwati da aka maki da sunan “Bincika” ko kuwa “search” da turanci a samar mabincikar bayanai. Ku shigar da wani darasi. Ku latsa ku bincika domin ku nemo makala dake dangantaka. Kuma zaku iya rubuta cikakken tambayoyi kuma ku samo amsa. Ku kokarin karanta amintaccen yanar gizo gizo kawai. Da yawan amintaccen yanar gizo gizo nada cikakken shafi dake magana akan su. Kuma galibi ana yawan samun su a farkon shafin su idan muka bincika. Kada mu dogara akan bincike domin samun amsa masu muhimmanci kamar tambayoyin asibiti. Ku naima wani kwararre a ungwanku ku tambaye su irin tambayoyin nan.

Yin amfani da shafukkan sada zumunta

Kun taba ganin wannan karamin tambarin na’urar kwamfuta a nan kasa a wani shafi? Toh wannan shafin na kan Facebook da kuma sauran shafukkan sada zumunta. Idan muka latsa muka rarraba muna da daman raba abun da muka karanta a Facebook din mu ko kuwa sauran shafukkan sada zumunta. Idan muka latsa haka yana nufin zamu iya bin shafin yanar gizo gizo a Facebook domin mu riga samun sabunta ko labarai irin wannan a shafukkan mu. Ku tuna cewa zaku rarraba abubuwa da zai taimake mutane ne kawai ko kuwa ya saka su farin ciki. Kada ku rarraba ko ku saka abubuwa kamar gulma ko labarai masu fitsara.

facebook_like.jpg

Ku ajiye shafukka

Bayan kun nema wani yanar gizo gizo da kuke so, karshen abun da zaku so shine ku batar dashi. Ku duba madubin mazaba a mabincikar bayanai. Ku latsa akan “save as bookmark”. Ko mai yiwuwa zai ce “save page,” ya dangana da na’urar ku. Zaku iya bawa shafin wani suna na musamman domin ku iya tunawa. Zaku iya duba dukka shafukkan da kuka ajiye. Kawai kuje wajan mazabar sai ku latsa akan ma’ajiyar shafukka.

Rarraba

Wasu shafukka basu nan hade da shafukkan sada zumunta. Toh ya zamu rarraba su? Zaku iya kofin adireshin yanar gizo gizon da yake samar mabincikar bayanan (galibi yana farawa da https://) sai ku tura wa abokan ku ta Whatsapp, ko wasikar lantarki, ko kuwa sakonnin rubutu.

Zaku iya kofin adireshin daga samar mabincikar bayanai (galibi yana farawa da https://) domin ku rarraba. Ku manne adireshin a sakonnin rubutu idan kuna son mutane su ziyarta wannan shafin. Gaya mana wannan abun sha’awa na karshe da kuka samo a yanar gizo gizo. Kuma ku tuna ku ajiye a ma’ajiyar shafin Springster idan kuna son wannan yanar gizo gizon kuma kuna son ku cigaba da ziyarta.

Share your feedback