Jagorori na shugaba mai gagarumi

Dabaru akan yadda zaku jagoranta da kyau

Ke ce babban yarinya a gidan ku?

Ke ce shugaban ajin ku a makaranta?

Ko kece wanda abokai ke sa rai ki jagorantar su?

Ya kuke bi da irin wannan matsayin?

Akwai wani sanannen ruwaito dake fadin “ Karfin iko na cin hanci, cikkaken karfin iko na cin cikakken hanci”. Ma’anar shine, wasu lokuta kasancewa da karfin iko zai iya saka ku aikata abubuwa a wani hanya da bai dace ba.

Yawanci lokuta kasancewa shugaba zai iya yin kyau. Kuna da damar iko.

Kuna da ikon bawa mutane doka. Ba wanda zai tambaye ku.

Zaku iya bawa kannen ku dokar yin dukka aikin gida. Idan kuka ga dama zaku iya cin dukkan naman daya kammata ku raba da kannen ku.

A matsayin shugabar kungiyar ku, zaku iya yanke shawara ku dauka matsayin jogaranta koda yaushe.

Kuna ganin zaku iya cin nasara da dukkan wadannan domin kunyi girma ko kuwa kuna matsayin shugaban.

Gaskiyar shine babu abun dake madawammi.

Kasancewa shugaba akan hadin kai ne. Akan neman hanyar da zaku samu goyon baya daga wajan mutanen dake bin ku. Ana girmama shugaba ne ba tsoron sa ba.

Kamar shugaba ko kuwa babban yaya yakamata kuyi bauta. Yakamata ku nuna wa mutanen dake sauraran ku yadda zasu inganta rayuwar su.

Shugaban kwarai bata tsangwama ko daukan halakin mutane dake karkashin ta.

Shugaban kwarai baza ta zage matsayin ta ba.

Shugabannin kwarai nada hadin kai kuma suna bawa sauran yan kungiyar dama su dauke wani matsayi. Ba kulun suke yin komai ba.

Ku bi da mutane a yadda kuke so su bi da ku.

Ya kuke bi da kannen ku a gida? Kuna son yadda yan uwan ku ke bi daku? Kun san wani dake cin zalin ku saboda matsayin su? Kuyi mana magana a sashi sharhi.

Share your feedback