Kuyi farin ciki kuma ku gamsu
Kuna tunanin yin soyayya? Ba ku kadai bane! Yin soyayya al’ada ce a yin girma. Kuma zai iya zama abun nishadi!
Amma, yafi ku kasance a soyayyar dake da tsaro da kuma lafiya. Wanda kuke farin ciki da gamsuwa. Wanda zaku iya walwalar da kanku.
Wadannan dabarun zasu taimake ku farawa:
Ku zama abokai
Ana gina soyayya mai kyau da yarda, bi da juna daidai, da kuma girmama juna. Idan kuka fara da abokantaka, wadannan abubuwan zasu zo da sauki. Saboda zaku kara sanin juna kamar mutane tukun, kafan wani abu ya biyo baya. Mafi alherin shine, zaku sani ko kuna da abubuwa ko ra’ayi da kuke so tare. Kuma zaku iya sanin ko wannan mutumin na girmama ku da yaben ku a yadda kuke.
Kuyi magana
Idan kuna nan da wani, ku sake kuyi hulda dasu Idan akwai abun dake damun ku, zai fi kuyi magana akan sa a maimakon yin shiru. Saboda haka, daga ra’ayin ku zuwa shaukin ku, ku fito fili kuyi magana. Masoyan ku baza su iya karanta abun dake zuciyar ku ba. Ku fito sarai, ku fadi gaskiya koda yaushe.
Kada ku zama sirrin kowa
Daya daga cikin abubuwa masu kyau a soyayya shine idan kuka hadu da iyali ko abokan juna! Idan baza ku iya gaya wa abokan ku cewa kuna fita da wani ba, toh akwai matsala. Yakamata ku iya gabatar da abokan ku wa juna. Zai iya nuna wa muku matsayin ku a rayuwar juna. Banda wannan, zaku iya gano ko abokan ku na farin cikin soyayyar. Idan suna yi, toh madalla!
Ku samu lokaci wa kanku
Kasancewa a wani soyayya da wani baya nufin cewa dole ku kwashe lokaci tare koda yaushe. Kuna bukatan naku lokacin. Kada ku share abokan ku saboda kuna soyayya. Ko kuwa ku daina yin abubuwan da kuke so. So daya a dan lokaci, ku dan dauki hutu kuyi abun da kuke so. Akwai farin ciki a kasancewa ku kadai ma.
**Ku kasance da hankali da kuma goyon baya
Banda zagi ko kuwa share juna. Banda yin ihu ko duka – Koda ya kuke haushi. Koda yaushe ku goya wa juna baya. Kuyi imani da muradin juna kuma ku kawo wa juna farin ciki. Eh, baza ku yarda da juna koda yaushe ba. Amma zaku iya shawo kan matsalar ku da adalci da kuma hikima.
Ku tuna, kuna cancantar jin tsaro, kauna, da kuma yarda. Kuna da ikon fita daga wani soyayya idan kuna bakin ciki ko kuwa idan babu tsira. Idan kuna da damuwa sosai akan soyayyar ku, kuyi magana da wata ko wani amintaccen babba nan take.
Kuna da wasu dabarun soyayya?
Ku rarraba damu a sashin sharhi.
Share your feedback