Suna mun dariya

Kada ku bari ya raunata

Akwai wasu lokuta da wasu mutane zasu fadi abubuwa ko kuwa su aikata abubuwa a hanyoyi da zasu raunata ku.

Kamar yin cizgili game da siffar kan ku. Yin dariyar yadda kuke saka kaya ko kamanin ku.

Wasu mutane zasu yi dariyar ra’ayin ku da kuma muradin ku. Idan kuka gaya musu kuna son ku zama likitar fida, ko likitar hakori, ko kuwa injiniya, zasu yi muku izgili. Mai yiwuwa ma su gaya muku abubuwa kamar “Ba zai iya yiwuwa ba”.

Halayyar su zai iya shafin tabbacin ku.

Gaskiyar shine mai yiwuwa baza ku iya iko da yadda mutanen nan ke nuna halayyar su gare ku ba. Duk da haka zaku iya yanke shawara cewa baza ku saka ya dame ku ba. Eh, idan suka muku dariya yana raunata ku. Amma baza ku iya zuwa kuna fada da kowane mutumin daya muku izgili ba.

Ba lallai sai kun ga kanku a yadda suke ganin ku ba.

A nan gaba idan suka muku izgili. Ku gaya musu yadda abun ke saka ku ji. Zaku iya fadi da hankali “ Gaskiya bana jin dadi da kuke kira na doluwa, yana saka ni bakin ciki”

Idan mutumin ya cigaba da yin muku izgili, ku kai rahoton su wajan wani amintaccen babban mutum kamar iyayen ku ko kuwa yayin ku da zasu iya musu magana.

Wasu lokuta zaku iya juya kalmomin su masu raunata zuwa wani abun wasa. Ga misali, Idan suka kira ku mai katon kai zaku iya cewa “oh ai dan ina da kwakwalwa sosai ne”, idan suka ce kuna da katon idanu ku ce, “ saboda kuna son ku ga duniya ne”.

A ta nan, zasu san cewa kalmomin su basu dame ku ba. Zai nuna musu cewa baza su iya yin amfani da kalmomin su ko kuwa ayyukan su su saka jin bakin ciki ba.

Kada ku bari abun da mutane ke fadi ya yi kafiya da asalin ku. Suyi dariya, ba zai canza yadda kuka hadu ba.

Kun taba samun kanku a wannan al’amarin? Gaya mana abun da kuka yi a sashin sharhi.

Share your feedback