Abubuwa guda uku da muka san cewa baku taba yi da iyalin ku ba

Nishadi mai gamsarwa

Kwashe lokaci da iyali shine mafi kyau. Muna saduwa da iyaye da ‘yan uwa. Muna labarai da dariya da kuma shakuwa. Amma yana iya zama gundura idan ana maimaita abu daya koda yaushe.

Ga wasu abubuwar nishadi da zaku iya yi:

Kuyi wasannin allo
Wata hanyar walwalawa ne! Daga Ludo zuwa dara, akwai abubuwa da yawa da zaku iya zaba. Kuma mafi ingancin? Zamu koya wani sabon abu akan iyalin mu. Mai yiwuwa mu gano cewa mahaifiyar mu nada wani kwarewa. Ko kuwa kanin mu na son cin nasara. Dukka wannan zai iya saka mu shakuwa dasu. Da kyau, ko?

Kuyi Liyafan cin abinci
Wasu lokuta muna mantawa yadda halittar Allah keda kyau. Mu kwashe kwando da abinci, abin sha, da kuma abun ciye-ciye kamar Gala, ko biskit da chin-chin. Sai mu naima waje mai kyau wa liyafan cin abinci da iyali. Zai iya zama wani wajan shakatawa. Ko kuwa kowane wuri mai shiru a al’ummar mu. Kasancewa kusa da halittar Allah na taimakon mu daga shagaltarwa. Baza ma muyi tunanin yin labari a kan waya ko aika sakonnin rubuce-rubuce. Wannan yana nufi cewa zamu iya bawa iyalin mu dukka hankalin mu. Mu samu daman yin wannan, Yan Springster!

Mu kali hotunan iyalin mu
Abubuwa masu ban mamaki na faruwa idan muka tuna da baya. Mu dauka wannan tsohon ma’ajiyar hotuna iyalin mu dake daki. Sai mu tattara iyalin mu tare muyi kallo. Zamu iya yin wa mahaifin mu dariyar tsohon gashin sa da yake makaranta. Muyi sha’awar hotunan mu da muke kanana. Mu tsokane mahaifiyar mu akan rigar ta. Muna da su tunani masu ban mamaki a shekaru da suka wuce. Yana da kyau mu kalle su koda yaushe.

Kuna kwashe lokaci da iyalan ku? Me kuke yi? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback