Ku dauke gasar amsa tambayoyi
Tsokanan juna da kuma yin wasa akan komai. Ku da abokan ku na yin sa a kowane lokaci. Kuma a shafukan sada zumunta, kuna kirkira abubuwa masu kyau: hotuna, bidiyo, da sauran abubuwa masu nishadi. Amma idan baku maida hankali ba, zaku iya raunata wani da irin abubuwan da kuke sakawa.
Kada ku damu. Wannan gasar mai nishadi zai taimake ku yanke shawara ko ku saka abu ko kada ku saka. Mu fara:
Halin da kuke ciki: Kuna son ku saka wani abu da zai iya izgili abokan ku.
Tambaya na daya: Abun da kuke so ku saka ya ambaci wani abu dake saka abokan ku rasa tabbaci? kamar mai yiwuwa tsawon su?
A. A’a (A je tambaya na biyu)
B. Eh (daina)
Yin wasa da rashin tabbacin wani hanya ne mai sauki da zaku iya raunata su. Zai iya jawo tashin hankali da kuma bakin ciki. Zai fi ku guje irin wadannan abubuwan.
Tambaya na biyu: Abun da kuke sakawa na dauke da sirrin abokan ku ko kuwa hotunan su?
A. A’a (A je tambaya na uku)
B. Eh (Dagata)
Wannann bai dace ba saboda zai iya saka abokan ku a cikin matsala. Baza ku so su zama abun dariya ba a yanar gizo gizo. Banda haka, bai dace a rarraba bayanai masu sirri daba naku ba.
Tambaya na uku: Abun da kuke sakawa na dauke da kalmomi masu cin zarafi?
A. Mene? A’a! (A je tamabaya na hudu)
B. Eh (Tsaya)
Kalmomi zasu iya saka mutane bakin ciki. Mu saka shafukan yanar gizo gizo su zama wajen farin ciki ta kalmoni masu kyau. Ku baza kauna kowane rana.
Tambaya na hudu: Kun tabbata abokan ku baza suyi fushi da wannan ba?
A. Na tabbata sosai (A je sakamako na A)
B. Ban tabbata ba ( A je sakamako na B)
Sakamako na A: Ku saka!
Bai yi kama da wani abu mai lahani ba. Jeki ku tura.
Sakamako na B: Dakata!
Ku saka kanku a matsayin su. Idan suka muku haka, zaku ji dadi? Zaku yi fushi dasu? Ya kamata wannan ya taimake ku yanke shawara.
Toh gashi nan yan mata. Ku tuna, koda kuna wasa ne kawai, koda yaushe kuyi amfani da shafukan yanar gizo gizo da girma.
Toh, abokan ku sun taba saka wani hoton ku da baku so ba? Ya kuka bi dashi? Ku raraba da mu.
Share your feedback