Hotunan nada yawa? Eh ko a’a?

Ku kula da wadannan boyayyar hatsarin

Sannu Babban Yaya,

Da gaske ne wai babu kyau a saka hotunna da yawa a shafin yanar gizo gizo? Dukka abokai na nayi, amma malamar mu a makaranta tace zai iya jawo hankalin wani mai kutse. Me take nufi? menene yiwuwar aukuwar sa?

Da godiya,

Ban tabbata ko da wa zan imani ba


Sannu Mara tabbata,

Wannan tambayan nada kyau! Mai yiwuwa mutane su samu ra’ayi dabam a kan wannan.

Idan aka ce mutum dake kutse, ana nufin wani dake abu ko shigan wani waje ba tare da izini ba. Ko kuwa wani dake takurar mutane. Kun san cewa fasaha ya bawa kowane irin mutum daman samun kala kalar abubuwa akan ku daga hoto daya kawai.

Za’a iya yin amfani da duk hoto da kuka dauka a nemo ku. Kowane mutum zai iya bincike ya san inda kuka yi makaranta, ko kuwa inda kuke zama daga hoton ku.

Zasu iya neman ku idan baku kashe gurin da kuke ba a wajan yin seti (wannan setin ne ke bawa wayar ku daman rarraba bayanai akan inda kuke).

Domin ku tsira, yana da kyau ku kashe wajan dake nuna gurin da kuke a wajan seti a wayar ku, da kuma shafukkan sada zumuntar ku kamar Facebook, Instagram da kuma Twitter.

Ku kula da irin hotuna da bayanai da kuke saka wa a shafin yanar gizo. Ku tabbata cewa gurin da kuke ya zama na sirri. Baku san wanda ke kallon ku ba!

Zaku ga kamar malamar ku na damun ku ne. Amma ba haka bane. Malamar ku na son ku tsira ne, kuma ni ma ina son haka.

Da kauna,

Babban Yaya.

Share your feedback