Dakatawa na da kyau

Jira dan kadan nada kyau kuma

Idan muna girma muna samun sha’awar wasu abubuwa.

A wannan shekaran, ba komai bane idan kika dauka burin sanin samarai da jima’i.

Wasun ma nada abokai masu samarai. Kuma baza su daina yin magana akan masaniyar su ba.

Mai yiwuya zai sa mu ji kamar an bar mu a baya. Hakika zai kara sa mu son sani da yawa.

Kafan ki yanka shawarar, ga wasu abubuwa da zaki yi tunani akai;

  • jima’i zai iya jawo daukan ciki da wuri
  • jima’i zai iya jawo miki cutar jima’i. Kada ki manta da kanjamau. Duk da yake ana bada shawara ayi amfani da kwaroron roba domin mu kare kanmu daga cutar jima’i, duk da haka baza su kare ki gaba daya ba. Hanya guda da zaki yi jima’i mara matsala shine idan kika guje jima’i.
  • Yin jima’i kafan sassan jikin ki daya shafa jima’i suka bunkasa zai iya jawo miki wani abu mai hadari. Zai iya jawo miki lamari babba na lafiyar jikin ki.
  • Jima’i na zuwa da shauki sosai. Kin shirya wa wadannan abubuwan shauki dake zuwa da jima’i? Idan soyayyen bai yi aiki ba bayan jima’i fa? ya zaki ji? Idan abokin harkan ki bai maida miki kawazuciyar ki bayan jima’i fa? zaki iya jurewa?

Ke daya kika san lokacin da kika shirya daukan matakin nan. Idan baki shirya ba, zaki iya cewa a’a. Kada mu sake mu yarda wani ya matsa mana lambar yin abun da bamu son yi.

Kin san cewa yana da kyau ki dakata? Kin yarda cewa dakatawa nada kyau? Gaya mana dalilin da kike tunanin dakatawa nada kyau a sashin sharhin mu.

Share your feedback