Lokaci ya kai da zamuyi magana
Kuna kasa bude baki kuyi magana akan wasu abubuwa?
Kuna tsoron yin magana?
Mun san cewa akwai wasu maganganu da zasu iya yin wuyan yi. Amma, akwai abubuwa daya kamata kuyi magana akai. Abubuwa da suka shafe rayuwar ku na gaba, samari, ko kuwa jima’i.
Kun gani, fadin abun dake zuciyar ku nada muhimmanci.
Wannan ne ya saka muka dauki nau’in rarrba wadannan dabarun da zasu taimake ku yin magana.
Kada ku damu idan aka kira ku masu surutu
Yawancin lokuta, a matsayin yan mata, ana koya mana mu kasance da hankali, sanyi da kuma tarbiya. Ku manta da wannan - Yan mata ma nada yancin fadin ran su kamar samari.
Wasu lokuta idan muka fadi ran mu, wasu mutane zasu ce kuna da yawan surutu.
Gaskiyar shine, kuna bayana yadda kuke ji ne kawai ko kuwa abun da kuke so. Kada su sake kuji kamar kuna bukatan boye kanku domin ku gamsar da wasu.
Ra’ayin ku nada muhimmanci
Babu wani a duniya da zai iya dauki matsayin ku! Ku san wannan. Saboda haka kuna bukatan yin tabbaci da muryan ku.
Kuma kuna bukatan koyan cewa ra’ayin ku nada muhimmanci, a kowane al’amari. Idan kuna son ku maida hankali a makaranta a maimakon yin soyayya kamar abaokan ku, to kuyi! Idan kunfi son wakar turawa fiye dana hausa, toh da jin sa.
Share your feedback