Wanda lokaci ne ya kamata nayi magana?

Kada kiyi shiru, Kiyi magana…

Tunanin ku (3)

Kiyi tunani ki saka kanki a wani aji. Kina karanta wani takarda sai kika kala taga kika lura wani dan ajin ku na karban kudi daga wajan wani dan kankanin yaro. Yaron na kuka yana rokan dan ajin ku ya bar mishi kudin.

Me zaki yi a wannan al’amarin?

Idan ana tsangwamar wani dake kusa da ke zaki fadi wani abu ko zaki yi tafiyar ki?

Toh idan wani ya raunata ki ko kuwa aka tsangwama ki fa?

Zaki yi shiru ko kuwa zaki gaya wa wani?

Yawancin mu na fuskance irin wannan al’amarin. Idan wannan ya faru, yawancin mu na tsoron yin magana. Wasu lokuta wani ya taba yin mana barazana. Ko kuwa muna tsoron mutane baza su yarda da mu ba. Ko kuwa idan yayi muni, zasu daura mana laifin.

Amma kamar yan Springster kina bukatan koyan yin magana. Wannan saboda rashin yin magana zai iya sa al’amarin ya sake faruwa kuma idan ya cigaba zai iya kara muni.

Kuma, idan muka bar mutane suka cigaba da yin abubuwa mara kyau da suke yi, zasu iya yin wa wani.

Saboda haka kamar yan Springsters mu koya yin magana idan;

  • wani abu bai dace ba
  • wani mataki ya saka ki jin wani iri
  • wani yana miki barazana ko yana ma wani barazana
  • ana raunata ke (ko wani), ko ta jiki ko kuwa ta shauki

Wasu lokuta zaki iya jin tsoro cewa wanda kika yi wa magana ko kuwa wanda kika yin magana akai zai iya raunata ki domin karfin halin ki.

Idan wannan ya faru kiyi tunanin wani babban mutum da kika yarda da kuma wanda kika san cewa zai iya kare ki a kowane lokaci sai kiyi masa/mata magana a cikin sirri. Idan baza ki iya tunanin wani kamar haka ba ki tambaye wata abokiyar ki ko ta san wani kamar haka da zaki iya yin wa magana.

Zamu so idan zaki iya gaya mana yadda kika yin magana a da kuma wanda kika yin wa magana idan wani abu mara kyau ya faru dake a wajan sharhi a nan kasa.

Share your feedback

Tunanin ku

Kawai Sai Inyi Hiru

March 20, 2022, 8:01 p.m.

Fatan Alheri

March 20, 2022, 8:01 p.m.

Fahtan Alhere

March 20, 2022, 8:01 p.m.