Da wa zanyi magana akan samari?

Samun shawara mafi kyau akan soyayya

Akwai yaron da kuke so a al’ummar ku?

Akwai samari dake tashin ku?

Baku tabbata abun yi akan su ba? Baku tabbata wanda zaku iya yin wa magana ba?

Kuna tsoron yin magana da mahaifiyar ku ko kuwa yar uwar mahaifiyar ku? Kuna damuwa zasu tsawata ku idan kuka yi magana akan maza?

Ko kuwa kuna tunanin baza su fahimce yadda kuke ji ba?

Toh idan muka gaya muku mahaifiyar ku ko yar uwar mahaifiyar ku ta fahimce yadda kuke ji fa.

Eh, wannan mahaifiyar ko yar uwar mahaifiyar naku da kuke jin tsoron yin wa magana akan maza na sane da abubuwa sosai akan maza.

Su ma matasa ne a da. Maiyuwa suma sun yi sha’awar samari da suke matasa.

Sun san abu daya ko biyu akan samari da soyayya. Suna son abu mafi kyau muka kuma galibi zasu gaya muku gaskiya.

Wannan ne dalilin daya sa yake da kyau kuyi musu magana.

Wanda zaku yi wa magana kafan ku yanke shawara nada muhimmanci.

Baza ku iya samun shawara daga wajan kowane mutum haka kawai ba, domin suna da girma ko kuwa suke kusa da zaku iya yin wa magana.

Yakamata duk wanda kuka zabi kuyi wa magana nada biyu daga cikin wadannan;

- Amintacce
- Masaniya
- Mai Shekaru
- Ba mai hukunta

Ku zabi wani da zaku iya walwala da, wanda kuke sha’awa da girmamawa. Zai yi muku sauki kuyi musu magana.

Ya kamata ku zabi wani da ba zai hukunta ku ba. Baza ku so wani da zai saka ku ji kamar “yara mara da’a” domin kuna son wani yaro.

Kuna bukatan wani da masaniya. Maiyuwa wata amintaccen babban mace mai aure.

Ba sai kun je wajan wata da kuka sani kowa na zuwa domin shawara ba. Ku zabi wata da zaku iya walwala kuyi magana da,wata da kuka yarda da da kuma kuke sha’awa. Zai iya zama babban yar uwar ku, ko Yar uwar mahaifiyar ku, ko babban dan uwar ku, ko wata mallama,ko wata mai bada shawara, ko kuwa shugaban wani kungiya. Wata dake nan kamar mai koyin yan mata a al’ummar ku.

Wa zaku so kuyi wa magana, mahaifiyar ku dake da shekaru, da masaniya da kuma kuka yarda da ? Ko kuwa abokan ku da basu da masaniya kamar ku amma zaku iya labari da?

Wa zaku so kuyi magana da akan samari? Kuyi mana magana akan su a wajan sharhi.

Share your feedback