Baza ku iya gamsar da kowa ba

Kuyi abun da kuke son yi kuma kuyi farin ciki

A matsayin yar mace, al’ada ce kuso a karbe ku. Musamman idan kuna wani ungwa da baku da abokai. Ko kuwa wani sabon waje da ba wanda ya san sunnan ku.

Kwarai kuwa baza ku so a a bar ku a baya ba a wajan nishadi. Mai yiwuwa zaku so ku gamsar da yaran ungwan ku domin su so ku. Mai yiwuwa ma kuyi marmarin kasancewa babban abokan su domin ku riga kwashe lokaci tare. Kuma babu komai da wannan.

A wani lokaci, dukkan mu mun taba al’ajabin ko kowa na son mu. Yana faruwa koda yaushe. Amma abun shine, baza ku iya gamsar da kowa ba. Ba wanda zai iya. Kowanne mu nada musamman. Muna da ra’ayi daban daban; shiyasa bamu amincewa akan komai.

Amma, duniya babban waje ne mai ban mamaki. Yana nufin cewa idan wani bai karbe ku a yadda kuke ba, akwai wasu da zasu yi. Zaku samu abokan arziki dake son ku da kuma girmama ku.

Saboda haka ku guje yin abubuwa da zai hana ku walwala domin kuna son ku gamsar da mutane. Baku bukatan amincewar kowane mutum domin kuji dadi. Kun hadu a koda yaushe, a kowane rana– Koda menene wani ya fadi.

Koda yaushe kuyi abun da zai kwantar muku da hankali. Idan baku son kuyi rawa, kada kuyi. Idan zaku so ku karanta wani littafi a maimakon buga wani wasan lido, kuyi sa. Farin cikin ku da kwanciyar hankalin ku shine mafi muhimmanci.

Idan kuka daina kokarin gamsar da mutane, zaku iya maida hankali a abubuwa masu muhimmanci. Misali, muradin ku, iyalan ku, da kuma lafiyar jikin ku. Ku tuna, mutum daya ne ya kamata ku gamsar da: shine kanku.

Kuyi rayuwar ku da kyau. Zamu goya muku baya. Kuma baza ku taba al’ajabin ko muna son ku ba. Saboda muna yi.

Kun taba gwada gamsar da kowa? Yaya kasance? Ku rarraba damu!

Share your feedback