Ki Kulla kyakkyawan kawance a rayuwarki

Kina da kawaye da yawa a yanar gizo fiye da wadanda kike da su a fili? Koyi yadda ake kulla kawance na hakika yanzu

Wayar salularki da yanar gizo da kwamfuta duk suna da muhimmanci! Za ki iya haduwa da wasu mutanen, ki koyi sababbin abubuwa ku kuma yi musayar ra'ayi da abokanai a duk fadin duniya. Amma ya kawarki da take makotaka da ke kuma? Yanar gizo akwai nishadi amma fa idan amfani da yanar gizo yana hana ki mu'amala da kawayenki na fili, to watakila zai fi kyau ki ajiye waya ki fara amfani da nofilter!

Magana ta zahiri

Amira Dalibar Sakandire ce 'yar shekara 16 ta ba mu labarin lokacin da ta je wani dandali da take sha'awa ranar Asabar. Dukkanin kawayenta suna wajen, amma ita kadai ta yi shirusai karar sautin hira ta waya kawai kake ji daga wayar kowa. Wurin wani abin dariya, sai wata kawarta da ke zaune kusa da ita ta turo mata da sako!

Ai sai ka ji kamar wasa amma fa da yawan mu mun taba samun irin wannan. Idan kana jin kewa ko da kuwa kana tare da kawayenka ne, to ga wata dabara - ku yi wani wasa duk wadda ta fara duba wayarta idan kuna tare to sai ta yi wa kowa wakar ban dariya, ko kuma sai ta yi wani abu na jin kunya. Idan hakan bai sa kawayenki suna ajiye wayoyinsu ba, to ba abin da zai sa su su ajiye.

Rayuwa ta zahiri

Muna kaunar yanar gizo - akwai kuma bubuwa da yawa da za mu koya mu kuma yi tunani a kai a yanar gizo. Idan kuma kika rasa abin yi a google, akwai kuma hotuna masu ban dariya!

Kada ki taba mantawa da abu mai muhimmanci, wato mutanen da kuke tafe da su. Kawayenki. Danginki. Wadanda kika damu da su. Ki mayar da hankali ga rayuwarki ta zahiri don ki samu abin da za ki yi sha'awa ki kuma yada a rayuwa ta zahiri ma.

Share your feedback