Ki Na Cikin Mummunan?

Zabi Abokan Arziki Don Jin Dadin Rayuwa

Tunanin ku (5)

Zaɓi ƙawayenki cikin dabara. Gewaye kanki da mutanen kirki waɗanda za su ƙarfafeki ki ci gaba da ƙoƙari ko da ana kashe miki karfin gwiwa. Nisan ci ƙawayen da suke miki dariya ko kuma neman dakushe ki. Yi cuɗanya da waɗanda ke son kyawawan abubuwan da ki ke yi. Zaɓi ƙawaye masu son ilimi da karatu a makaranta, masu son samun sakamako mai kyau da ƙirƙirar damammaki domin kansu. Ma su kyakkyawar buri a rayuwar su – tamkar yadda ki ke da buri! ƙawa ta arziki ita ce wadda ki ke ƙauna kuma ki ke tallafawa a duk halin da ake ciki. Kuma su ma su na iya tallafa miki haka. Ƙawaye na arziki haƙiƙa na da alƙibla da kuma hangen nesa domin rayuwarsu. Ƙawaye na taimakawa juna wajen kaucewa ɗaukar mummunar shawara wadda za ta kawo masu cikas ga rayuwarsu a gaba. Zamo ƙawa alkhairi. Ki zamo mai gaskiya da tallafawa, kuma ki zama abar gasgatawa. Ku taimakawa juna, kuma ki yafewa ƙawa wadda ta yi kuskure.

Share your feedback

Tunanin ku

Hello

March 20, 2022, 8:03 p.m.

Ina Ƙaunar Mai Ƙaunata

March 20, 2022, 8:01 p.m.

So Abun Alfaharina

March 20, 2022, 8:01 p.m.

Hello

March 20, 2022, 8 p.m.

Thanks

March 20, 2022, 8 p.m.