Kina Jin Ka' daici a Duniya?

Ga Yadda Za Ki Jure

Tunanin ku (2)

Za ki iya jin kaɗaici koda komai yana tafiya dai dai a hanyarki. Mai yiwuwa ke kaɗai ce kuma ba ki da zaɓi a kan wannan, ko kuma ba kya jin ki na tare da wata ƙungiya ko wani taro – ko kuma ba ki samu wani da zai fahince ki ba. Jin kaɗaici na iya barinki da miliyoyin tambayoyi. Me yasa ya faru? Laifi na ne? Wasu lokuta kaɗaici na iya sawa ki ji cewa ki na son ki daɗa janyewa to amma zai yiwu akwai mutane masu ƙoƙarin riskuwa da ke. A hankali zauna da mutane masu ƙaunarki a gewaye da ke. Samun mutane a rayuwarki waɗanda za ki yi magana da su na iya taimaka miki jurewa da rashin jin daɗinki da rashi. Zuwa wani lokaci za ki fara gasgata mutane kuma. Nemi ƙungiya masu tallafawa. Fatuma ta nemo Heshima Kenya kuma akwai wasu ƙungiyoyin tallafawa a ko wace ƙasa ta duniya waɗanda za su taimaka miki ki sake samun rayuwarki ta dawo gaba ɗaya. Yi tambaya a wajen ‘yan sanda, makaranta ko ki tambayi wani babba da ki ka sani domin taimaka miki nemi wannan kungiyar. Ba ke kaɗai ba ce. Ba kowa ke da dangi ba kuma akwai wasu ‘yan matan kamar ke. Za ki iya gina ƙaƙƙarfa dangantaka da kusantar mutane a garesu.

Share your feedback

Tunanin ku

hakuri maganin zaman duniya

March 20, 2022, 8:04 p.m.

MAHA KURCI MAWADACI YAR UWA

March 20, 2022, 7:57 p.m.