Ba ni da iyaye.

Amma ina da damammaki

Tunanin ku (1)
  • Da akwai mutane kusan miliyon uku da digo bakwai na kasar afrika ta kudu kusan rabi daga cikin su sun rasa iyayen su ta dalilin cutar kanjamau. Ga labarin daya da ga cikin ‘yan matan.*

Suna na Preity, shekaruna 20 kuma ina zaune a Afrika ta Kudu. Lokacin da na ke ƙarama ina zaune tare da gwaggona da kawuna. Sun saka ni na yi imani cewa su na da damar da za su dokeni kuma su cusguna min sabo da ni ba ‘yar cikinsu ba ce, kuma ba ni da wani wuri da zan je. An saka ni a tarko.

Muguntar da suka yi min a bayyane yake. Idan na tambayi gwaggona audugar mata idan na sami al’ada, sai ta ce: “Yi amfani da jarida!” Lokacin da na ke so in gyara gashina ya yi kyau, sai ta ce: Akwai ruwa da hasken rana, me kuma ki ke bukata…”. Abin mummuna ne.

Rayuwa ta yi min wahala a lokacin. An kashe min ƙwarin gwiwa. Sai bayan na gama aikace-aikacen gida masu wahala cikin dare, sannan ne zan ɗauko litattafan makaranta in yi ayyukan gida na makaranta.

Wata rana, bayan na yi tunani a kan haka na tsawon lokaci, na sami ƙwarin gwiwar da ya kamata na tafi na yi magana da ma’aikaciyar jin daɗin jama’a da na ji labari wajen malamarmu a makaranta. Na ji tsoro. Amma na yi farin ciki da yin hakan. Don ta canja rayuwata.

Lokacin da naje wurinta, na gaya mata labarina kuma na yi kuka na yi kuka. Ta kalli idanuna kuma ta gaya min, “Yarinya, BABU MUTUMIN da ya ke da dama ya dokeki ko ya yi miki mummunar ɗauka.” Ta tafi tare da ni zuwa gidana kuma ta haɗu da masu riƙona. Ta tattauna da su kaɗan. Ya ɗan ɗauki lokaci amma daga bisani ta taimaka min na sami wani wurin da zan zauna nesa da su. A can an kula da ni. Na sami damar mayar da hankali a kan karatuna, kuma na sami ƙarfi.

Lokacin da nake gidan gwaggona da kawuna ina jin tsoron neman taimako. Amma na yi farin ciki da na yi haka. A yanzu ina cikin farin ciki da lafiya. Ina mai alfahari kuma. Ni yarinya ce da na yi yaƙi domin fidda hakki na kuma na yi nasara.

Share your feedback

Tunanin ku

Ty sai ki dada godiya ga allah pe your comment here...

March 20, 2022, 8:01 p.m.