Labarin soyayya na Najeriya

Yin soyayya zai iya zama abun nishadi

Samari a al’ummar mu sunce ina tsorata su. Sunce bana yin murmushi kamar sauran yan mata. Sunce ina da girman kai sosai. Dukkan abokai na nada samari banda ni. Ban saka wannan al’amarin ya dame ni ba.

A yayin da abokai ne ke yin soyayya, ina taimakon mahaifiyata a kasuwa. Shagon ta na cike da aiki. Abokan kasuwanci ta na yawa kuma akwai abubuwan yi sosai.

A watan Afrilu daya wuce, wani yaro ya shiga shagon mu da yar uwar sa. Suna son su siyo madara. Na halarta su tunda mahaifiyata bata nan. Na lura cewa yaron nada hankali. Da yar uwar sa tayi kuskure ta fadar da madaran a kasa, bai yi mata ihu ba. Bayan da suke tafi, na kasa daina tunanin sa.

Bayan kwanaki suka wuce, ya kara zuwa shagon mu. A wannan lokacin, mahaifiyata na shago. Yana mata magana da mutunci. Yana ta bata dariya. Kawai, sai yazo ya same yace sunnan sa Daniel. Ya kale ni a cikin ido. Na gabatar da kaina sai na cigaba da aiki.

Dana kala sama, yana kan tsayiwa a wajan. Zuciyata ya fara bugu da sauri. Ya tambaye ni ko zai iya ziyarta ni. Ina jin kunya, amma sai na ce masa eh.

Kuma ya cika alkawarin sa, Daniel yazo da katin wasa. Munyi wasa har muka manta ko wa ke cin wasan. Ban damu ba. Naji dadin zama da yin magana dashi. Har na san cewa yana zama a dayan bangeren gari. Nayi mamaki cewa yazo daga waje mai nisa domin ya gan ni.

Muka fara kwashe lokaci tare sosai. Yace yana son yadda nake daukan kaina. Baya katse ni idan ina magana kuma kamar yana sha’awar ra’ayi na da muradi na. Yana taimako na a shago koda mahaifiyata ta gaya mishi kada ya damu. Da muka koma gida, tace yana da tarbiya. Naji dadin jin wannan.

Bada dadewa ba mahaifiyata tace zamu iya zuwa wani waje mu kwashe lokaci. Muka fara soyayya da gaske. Zamu iya zuwa wajan cibiyar matasa muyi wasa. Koda yaushe muna tabbata cewa muna wasa a wajan da akwai mutane. Wadannan samarin al’ummar mu suna mamaki. Suka saka wa Daniel ido kamar yana da kai biyu. Daya daga cikin su ya tambaye shi yadda ya saka ni na yarda na fita dashi. Daniel yayi dariya yace, “wannan sirrin mu ne”.

Kasancewa “abokai kawai” da maza na cikin yanki na yin girma. Idan kuna ji kamar kun shirya, ku zabi wani da zai bi daku da kyau, wanda zai so ku a yadda kuke, ya girmama ku da ra’ayin ku, wanda ba zai matsa muku kuyi wani abu da baku son yi. Akwai wani a rayuwar haka? Gaya mana a nan kasa.

Share your feedback