Shawarar Titi akan yadda yakamata a bi da ‘yan mata

Dukkan yan mata na cancancin a bi dasu da kyau

Tunanin ku (3)

Titi ta kamala karatun ta daga makarantar sakandare kuma tana da babban abu data tsara wa rayuwar ta. Tayi masaniyar abubuwa da yawa a shekaru goma sha takwas da suka wuce kuma tana jin kamar akwai wasu abubuwa da ta so wani ya gaya mata sanda ta fara balaga. Bayan nan, bata san abubuwa sosai akan samari ba da kuma yadda zata sani ko namiji na kaunar ta da gaskiya ne. Amma yanzu tana jin kamar ta koya abubuwa sosai kuma zata so ta taimake sauran ‘yan mata ta rarraba masaniyar ta.

Ga wasu siddabaru data rarraba da mu;

  1. KAUNA: Ya kola da yadda kike. Saurayi na kwarai baya watsi da ke. Yana kiran ki kuma yana tura miki sakonni. Idan yana zama a kusa dake, yana zuwa ziyartar ki. Yana son ya san yadda kike ji. Kuma yana murna ya saurare ki. Yana fadin abubuwa dake sa ki jin dadi.
  2. GIRMAMAWA: Dukkan mu na cancancin girmamawa. Bai kamata Saurayin ki ya zage ki ko ya miki duka ba. Koda menene ya jawo fadan. Idan yayi haka, ki karke abokantakan nan take. Kuma ki kai rahoton a wajan baligin mutum da kika yarda da.
  3. DARAJA: Bamu da farashi. Saboda haka ba wanda ke da izinin saka ki jin wani iri akan jikin ki. Yakamata saurayin ki ya so ki a yadda kike. Kada ya fadi abubuwa maras kyau akan kamanin ki, ko nau’in ki, ko kuwa jikin ki. Kina da kyau a yadda kike.
  4. ALHERI: Yakamata a bi da mu da hankali. Idan kina da aboki na miji dake kwashe lokaci da ke, zai lura ya taimake ki idan kina bukatan taimakon shi. Zai kuma yi magana dake idan kina da matsala. Titi ta gaya mana akan lokacin da uwar mahaifiyar ta ta rasu, tana ta bakin ciki. Taci nasara cewa abokiyar ta, Chuka, na nan kusa a kowane lokaci ta taimake ta samun sauki idan ta fara kuka.

Kina ji kamar akwai wasu abubuwa namiji mai hankali yake yi dake nuna cewa yana kaunar yarinya? Gaya mana a sashin sharhin.

Share your feedback

Tunanin ku

yayi kau

March 20, 2022, 7:58 p.m.

busuna

March 20, 2022, 7:58 p.m.

Soyayyar Gaskiya Batatsufa

March 20, 2022, 7:56 p.m.