Akwai wani matsala ne da ni?

Meyasa kowa ke mun dariya?

Kwanan nan, nayi masaniyar abubuwa masu wuya a makaranta. Sauran yan mata na cin zali na, domin bana kama dasu. Na kusa na shiga shekaru goma sha hudu - amma ina kama da mai shekaru goma!

Har suna mun dariya domin ban fara nonuwa ba ko kurajen fuska. Halayar su ya saka ni bincike kaina.

Akwai wani matsala ne da ni? Meyasa na banbanta da sauran yan mata?

Cin zalin yayi yawa har bana son naje makaranta kuma.

Wata rana na wayance kamar bani da lafiya. Na tsaya a gida na kwashe lokaci ina karanta labaran Springster.

A shafin ne na koya akan wani abu da ake kira balaga. Bisa ga Springster, lokaci ne da jikin mu ke fara nuna, ya zama jikin babban mutum da zai iya haihuwa. A wannan lokacin, jikin mace na kara bunkasa. Abun daya kama daga kwankwason ta zuwa cinya ta na kara girma. Mai yiwuwa ma ta fara masaniyar jinin al’adar. Mutane dabam na masaniyar balaga a shekaru dabam. A matsakaici, yan mata na masaniyar balaga a tsakanin shekaru goma zuwa goma sha hudu, wasu kuma na yi da sauri ko kuwa daga baya.

Hankali na ya kwanta dana gano cewa bani da wani matsala, ni cikakken mutum ce.

Koyan dukkan wannan ya koya mun nayi godiya da jikin da Allah ya bani. Ya saka ni gano cewa yin girma tafiya ne kuma kowa nada tafiya dabam.

Yanzu, ina kaunar jiki na kuma ina yin maganar alheri akan sa.

Saboda sabon bayanan, na samu karfin hali naje makaranta washe gari.

Kamar yadda suka saba, suka fara tsokana na. Amma wannan lokacin na tsaya da gaske na gaya musu da tabbaci cewa, “saboda ban fara jinin al’ada na ba, ko nonuwa da girmar duwawu baya nufin cewa jiki na nada matasala. Ina kaunar jikina kuma ina son na bari yayi girma kamar yadda ya kamata a lokacin daya dace”.

Bayan dana kare kaina suka daina tsokana na. Suka gano cewa na san abubuwa sosai akan balaga. Suna son su san inda na samo bayanan, sai na gaya musu, “Daga Springster!”

Idan kuna nan kamar ni, ina rokon ku dan Allah kada ku kwatanta kanku da sauran mutane. Kuyi shagali kuma kuyi godiya da jikin ku koda yaushe a yadda yake.

An taba tsokanan ku domin yadda kamanin ku yake? Ya kuka bi da al’amarin? Ku rarraba martanin ku da mu sashin sharhi.

Share your feedback