Innar ku ma nada ban mamaki

Blessing ta samu wata abokiya mai ban mamaki

A watar yuni daya wuce, mahaifiya na ta tura ni zama da Inna Uzo. A ranar dana ji labarin nan, nayi kuka.

Ba dan bana son Inna Uzo ba, amma saboda zan yi kewan iyali na sosai. Bamu taba rabuwa ba.

Yan uwana na saka ni dariya domin kada na damu. Mahaifiyata ta gaya mun na dan lokaci kadan ne. Tace zan dawo idan abubuwa suka kara sauki. Muka yi alkawari mu cigaba da zumunci.

A farkon mako da Inna Uzo, na kasa yin bacci da dare. Rayuwa tayi daban. Na rikice. A gida, na saba tashiwa da asuba, nayi karin kumallo. Amma a gidan Inna Uzo, bana yin abinci. Inna Uzo na son yin abinci da kanta.

A gida, bamu cin abincin dare tare. Kowa na aiki, saboda haka yawancin lokuta bamu zuwa gida a lokaci daya. Amma a gidan Inna Uzo, muna cin abinci tare kowane yamma.


A lokacin cin abinci, tana tambaya akan abubuwa sosai. Tana son ta san yadda nake kwashe lokaci a rana. Tana fatan ina hutawa lafiya. Har ta tambaye ni ko ina sha’awar wani yaro!

Ban saba bude ciki na wa kowa ba baya ga mahaifiyata da yan uwa na. Ina bukatan tambayan mahaifiyata abun yi. Sai na karbi aron wayar Inna Uzo na kira ta. Tace kada na damu, Inna Uzo kawai na kokarin kara sani na ne da kyau. Tace na walwala.

Bayan wannan, na fara tadi da Inna Uzo. Na koya abubuwa da yawa game da ita. Tana son wakokin Najeriya– Kamar ni. Tana rufe idon ta idan tana dariya.Bata bi dani kamar karamar yarinya.

Na fara zuwa cibiyar matasa da ita. Muna wasanni da kuma kwashe lokaci da sauran mutane. Bayan lokaci kadan, na gaya mata yana mun wuya na fadi abun dake zuciya na. Ta karfafa ni na samu karfin yin magana. Tace koda yaushe na ringa fadin abun dake zuciya na. Naji dadin yin amana da ita.

Bayan lokaci kadan, na koya cewa zan iya gaya wa Inna Uzo komai. Bata hukunta ni ko ta mun dariya. Tana bani shawara mai kyau. Na san cewa zan iya amincewa da ita koda menene.

Zama da Inna Uzo ya canza ni. Na kara zama mafi tabbaci. Har yan uwa na sun lura a waya. Dana koma gida, nayi farin cikin ganin iyali na a karshe. Amma na kosa na kara ziyarta Inna Uzo kuma. Innan mafi inganci har abada!

Daga iyayen mu zuwa yan uwan mu, iyali shine komai. Amma yan dangi kamar su Inna da kawu ma na gagarumi. Suna goyon bayan mu da kuma karfafa mu. Kamar

Inna Uzo ta nuna mana albarka.

Kun shakuwa da Innan ku ko kuwa Kawun ku? Me kuke so game dasu? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback