Na dawo kuma na kara inganci

Yadda na sabunta kaina

lokacin da nake shekaru goma sha hudu an kore ni gida daga makaranta. Iyaye na basu iya biya mun kudin makaranta ba.

Nayi bakin ciki. Nayi tunanin karshen sa kenan.

Wata rana, makwafcin mu Mr Nduka ya tambaye ni idan ina son na zama makaniki. Ya lura yadda nake yawan leka cikin shagon aikin shi.

Ina kaunar motoci. Amma ban taba tunanin zama makaniki ba.

Iyaye na basu yadda ba da farko. Amma a karshe sun yadda bayan Mr Nduka yace horon kyauta ne kuma da tsira.

Lokacin dana fara, ina ta kunya. Musamman lokacin dana ga yan aji na na dawowa daga makaranta. Wasu ranaku ina gujen su.

A shagon aikin, sauran makanikan da wasu abokan kasuwancin na mun dariya. Sun ce yar mace baza ta iya irin wannan aikin ba.

Na gaya wa mahaifiya ta. Ta gaya mun kada na kula da su.

Na yanke shawara na watsi da su na kara sa karfin aiki.

Wata rana, wata mata da tazo ta gyara mota ta gan ni.

Na burge ta. Ta tambaye ni akan abun dana tsara na rayuwa ta na gaba.

Na gaya mata ina son na koma makaranta.

Ta taimake ni rijista a makarantan yamma.

Shekaru hudu sun wuce da aka kore ni gida daga makaranta. Na kusa gama horo na a shagon makanikin.

Na daina jin kunya idan naga yan ajin mu. Wasu ranaku suna zuwa su gan ni a shagon aiki na. Wasun su naso su koya suma.

Na kammala karatu na a makarantan yamma. Na nema na karanta darasin anniyan inji a jima’i a shakara na gaba.

Na tsara cewa zan bude nawa shagon aiki a nan gaba. Ina son na horar da sauran yan mata.

Wasu lokuta, ina tunanin da na fid da rai. Da me ya faru da buri na?

Kina masaniyar lokaci me tauri? Kada ki fid da rai.

ki tuna cewa zai wuce. Zaki sabunta kanki.

Kiyi imani da burin ki. Koda sauran mutane sun ce baza ki iya ba.

Ki maida hankali a muradin ki. Idan kika kara aiki sosai zaki iya cin burin abun da kike so.

Gaya mana akan wasu hanyoyi da kika kawar da wani al’amari mai wuya.

Share your feedback