Zama mai yancin kai - Sashi na uku

Kada kuyi tafiyan ku kadai

Sannu Yan mata,

Ina ta rarraba labari na na zama mai yancin kai. Ban san ko kun ga sauran labarai na ba? Idan baku yi ba ku duba nan Zama mai yancin kai shashi na daya da kuma Zama mai yancin kai sashi na biyu domin ku karanta

Yan mata zaku iya tuna da wannan matsalar dana masaniyar a baya? Toh, na yanke shawara cewa ba zan fid da rai ba. Nayi imani da kaina kuma nayi tunani mai kyau game da sakamakon.

A maimakon fid da rai nayi wani abun mamaki. Na dauke hoton duka kayan hadin da suka zube a kasa. Sai na saka su a shafin Facebook dina na rubuta “Ina bukatan gasa burodi guda hamsin kafan washe gari amma bani da kayan hadi #DanAllahA Taimaka”.

Dana kai gida, naga na samu sakonnin da yawa daga abokai na da makwafta na suna cewa suna da sauran gari, madara, man shanu da sikari! Abun mamaki!

Wasun su ma suka zo gida su taimake ni hada komai domin mu shirya wa babban ranar kasuwa washe gari.

Idan na tuna da baya…..ina tunanin abun da me zan yi da ba dan abokai na ba?

A da ina tunanin kasancewa da yancin kai na nufin cewa zan yi komai da kai na ne. Amma ba haka bane.

Kun gani, tafiyan zaman mai yancin kai bai zuwa da sauki. Kuna bukatan abokai da zasu goya muku baya a gaba dayar tafiyan. Saboda haka, kada kuji kamar neman taimako zai saka mutane suyi muku kallon masu nauyi. Bai kamata kuyi masaniyar rayuwa da kanku ba.

Kafan ku fara tafiyar yanci kai ku tuna

  1. Kuyi kaunar kanku kuma kuyi imani da da abubuwa masu kyau game da kanku.
  2. Koda abubuwa sun yi tauri…..KADA KU FI DA RAI.
  3. Kada ku gwada yin komai da kanku. Ku nema abokai da iyalai da zasu goya muku baya idan kuna bukata. Wannan baya nufin cewa baku da yancin kai.

A karshe na iya kai burodin shagon a daidai lokacin kasuwa...na samu kudin kaina na farko. Nayi farin ciki.

Eh, ya dan dauki lokaci kafan na cimma burina, amma na koya abubuwa da yawa game da kaina da kuma asalin ma’anar yancin kai.

Kuna tunanin fara wani sana’a ko kuwa koyan wani kwarewa amma kuma kuna kasa cin nasara? Me kuka ganin kuke bukata domin ku ci nasara? Ku rarraba damu a sashin sharhi.

Share your feedback