Ku zabi abu mafi kyau gare ku

Yadda nace a’a wa aure

Shekaru na goma sha uku da wani yaro a al’ummar mu ya tambaye ni na aure sa. Wa zai taba tunanin wannan?

Wannan ya faru a shekaru kadan da suka wuce, bayan dana hadu da wani tsohon dan makarantar mu.

A ranar da muka hadu, yazo ya karbi sakamakon jarabawar sa na WAEC da kuma NECO. Muka fara magana har muka musayar lambar wayar juna.

A takaice dai mun zaba abokai. Muna magana da juna kowane rana a waya.

Abubuwa sun kasance da kyau tsakanin mu har sai wata rana daya ce;

“ Halima, ke yarinya mai hankali ne. Bai kamata ace mace kamar ki bata da saurayi ba, ko kuwa ta jira har sai ta kammala karatun jami’a kafan tayi aure. Kin san yanzu na kammala makarantar sakandare kuma na shirya yin aure. Ina tunanin muyi aure.”

Da farko na zato yana mun wasa ne. Shekaru na goma sha uku kuma nashi goma sha bakwai. Ya za’a yi ya zata cewa yara kamar mu sun shirya yin aure? Kuma na zata mu abokai ne kawai, shiyasa na kasa gane daga inda maganar auran nan ke zuwa.

Na gaya masa cewa ban saka rai na a aure ba yanzu. Hankalina yanzu na kan zuwa jami’i ne.

Amma bai ji dadin amsar dana bashi ba. Ya so ya saka ni bakin ciki, sai ya fara gaya mun nayi godiya ma cewa saurayi mai digiri kamar shi naso ya aure ni.

Maganar sa bai dame ni ba. Kawai dai na san cewa ba zan canza ra’ayi na ba.

Ya fara matsa mun lamba.

Kuma dana gaya masa ya daina yayi fushi dani sosai. A lokacin nan ne na san cewa dole nayi wa wani magana akan wannan al’amarin. Nayi wa yaya ta magana kuma ta taimake ni sosai. Ta bani shawara;

“Halima, aure ba karamin abu bane. Abu ne da zaki yi saboda kina son kiyi amma ba don wani ya tilasta miki ba.

Yana da kyau da kike da tsari wa rayuwar ki a shekarun ki. Kuma, ina baki shawara ki maida hankali a tsarin ki. Kina da sauran shekaru a gaban ki, aure zai iya jira.

Musa kuma, na bukatan sanin matsayin ki a zancen nan. Ya kamata ki gaya masa zaki yanke abokantakar dashi idan ya cigaba da matsa miki.

Ki tuna, ra’ayin ki ne. Ya kamata ki lura da kanki da kuma rayuwar ki na gaba. Duk wanda ba zai goya miki baya ba, ya tafi.”

Kamar yadda yar uwata ta bani shawara, nayi wa Musa magana. Amma ya nace akan zancen aure. Sai nayi barazanan kai rahoton sa idan ya cigaba da damu na. Ya lura cewa na daina kiran sa a waya da kuma yin tadi dashi kamar yadda na saba.

A haka ya daina damu na.

Saboda masaniya na, na koya muhimmancin yin tauri.

Shiyasa nake son na bawa yan mata shawara dake irin wannan al’amarin. Dan Allah ku naima taimako daga wani ko wata amintacciyar babba. Kuyi wa wani kawun ku, ko Innar ku, ko dan uwa da yar uwar ku magana.

Kuyi wa wani ko wata da ta kware magana. Wata da zata iya taimakon ku daukan shawara mai kyau.

Kuma ku koya yin magana. Ku saka yaron ko mutumin ya san matsayin ku.

Ba wanda ke da iko game da rayuwar ku da ra’ayin ku.

Akwai wani daya taba matsa muku kuyi wani abu da baku son yi? Ku gaya mana yadda kuka bi da su a wajan sharhi.

Share your feedback