Sannu Babban Yaya: Na rikice game da rayuwata na gaba

Ku nemo asalin kwarewar ku

Sannu Babban Yaya,

Ni ce shugaban kungiyar mawakin ungwan mu, har zuwa watan daya wuce. Ina kaunar sa sosai. Kowa na fadin cewa zan yi nisa. Nayi tunani zan cimma burina na zama mawakiya.

Sai Kawu na yace bai kamata yarinya mai tarbiya ta zama mawakiya ba. Nayi bakin ciki. Bana son wani aiki da ba’a girmama. Sai na daina haduwa da kungiyar mawakan, a maimako na yanke shawara na zama lauya. Suna kyau idan suka saka wannan farin hular gashin su da kuma bakar rigar su.

Wata rana, na karanta hirar wata sanannen lauya a yanar gizo gizo. Tace yana daukan shekaru da yawa a kammala karatun. Na san cewa ban shirya wa wannan ba. Shi yasa na canza ra’ayi na. Wannan lokacin, na yanke shawara na zama mahoriyar karnuka tunda ina kaunar karnuka. Dana gaya wa kawu na, yayi dariya saosai. Yace babu mahoriyar karnuka a kasar Najeriya. Naji kamar kasa ya bude ya hadiye ni.

Ni dai kawai ina son na samu burina, Babban Yaya. Amma bani da dabaru. Dan Allah ki taimake ni kafan na haukace.

Da godiya,

Leila.


Sannu Leila,

Da nake budurwa, ban tabbata abun da nake so na zama a rayuwana na gaba ba–Kamar ke. Kamar wannan bai isa ba, bani da kowa da zan yi wa magana. Saboda wannan, na yanke shawara cewa idan nayi girma, zan taimake yan mata domin kada su masaniyar abubuwan dana yi.

Idan na gaya wa mutane abun da nake so nayi, basu ganewa gabadaya. Suna fadin cewa ba aikin kwarai bane. Amma bana barin sa ya dame ni. Kuma yanzu gani nan yau!

Kin gani, babu matsala da rikicewa akan rayuwar ki na gaba. Yana faruwa da dukkan mu. Kije da hankali, yarinya.

Abun shine, gina wani sana’a zai iya wuya. Amma idan kina kaunar abun da kike yi, zaki yi farin ciki kuma baza ki ji kamar aiki mai wuya bane. Tunda kina son yin waka, ina murnar gaya miki cewa babu komai da kasancewa mawakiya. Kasancewa da tarbiya ba akan aikin da kike yi bane ko kuwa yadda kike saka kaya. Akan yadda kike bi da sauran mutane ne da kuma yadda kike rike kanki. Mata mawaka kamar Simi, Asa da kuma Omawumi na cin nasara. Kuma suna shawarta mutane da yawa. Saboda haka kada ki bari kowa ya hana ki bin burin ki.

Koda yaushe ki tuna, rayuwar ki naki ne. Kiyi abun da kike so, ba abun da mutane ke son kiyi ba. Baza ki iya gamsar da kowa ba– sai kanki. Saboda haka kiyi abun dake kwantar miki da hankali.

Kuma, akwai mahoran karnuka a Najeriya. Kawun ki na bukatan sanin wannan.

Ina fatan wannan zai taimaka!

Sannu,

Babban Yaya

Kuna da wani dabarun rayuwa na gaba? Gaya mana a nan kasa.

Share your feedback