Kada ki yarda matsi na zamani ya bada ma’anar ki

Yadda Fiyin ta ajiye tsohon kanta da kuma sabobin abokan ta.

Ranar farko na Fiyin a makaranta ya kasance da kyau. Farkon yarinyar da ta hadu da tayi mata murmushi tace, “sannu, sunana Hauwa. zaki iya zama a gefe na.” Fiyin ta hadu da abokan hauwa a lokacin wasa. Bada jimawa ba, Fiyin ta zama abokiya da dukkan su.

Fiyin bata da abokai a tsohon makarantar ta. Ta shiga da lati, kuma kowa ya riga ya hada abokantaka. Taji tsoro cewa abun daya faru a tsohon makarantar ta zai sake faruwa kuma. Fara’an Hauwa ya canza komai. Fiyin tayi murna sosai.

Fiyin na son ta shiga kungiyar rawa na bayan makaranta. Amma dukka abokan ta sun shiga kungiyar wasan kwaikwayo. Fiyin bata son tayi kewan abokan ta ko kuwa wani labari ya wuce ta. Sai taje ta shiga kungiyar wasan kwaikwayon.

Iyayen Hauwa yan kasuwanci ne da katon shago masu aiki sosai. Yawancin dare, basu kaiwa gida sai bayan karfe goma na dare. Shiyasa Hauwa ke samun ta fita da dare. Wasu lokuta, Hauwa da abokan ta sunyi maganan zuwa kasuwa da dare su kala kaya kuma su ci guru-guru.

Fiyin taji kamar an barta a baya. Mahaifiyar ta baza ta bari ta tsaya a waje bayan karfe shida na yamma. Tana son tayi yawo da abokan ta. Sai fiyin ta fara tunanin da zata gaya wa mahaifiyar ta. Amma tayi kusa da mahaifiyar ta sosai. Bata son tayi mata karya ko kuwa ta saka ta damuwa.

Fiyin ta yanke shawara cewa zata yi magana da mahaifiyar ta akan matsalolin ta. Tana son sabobin abokan ta amma tayi daban da su. Mahaifiyar Fiyin tace ita ma abu kamar haka ya faru da ita da take shekaru goma sha hudu. Ta yanke shawara cewa zata canza kuma abokan ta na gaske basu damu ba. Har sun bata sunan bogi – ‘Sade na musamman’. Sun ce ba kamar irin ta. suna kaunar ta domin wannan. Kuma sun cigaba da abokantakar.

Fiyin ta yanke shawara cewa zata bar kungiyar wasan kwaikwayon ta koma kungiyar rawa. Sai ta gaya wa abokan ta baza ta iya fita bayan karfe shida. Hauwa tace tana ji dama zata iya yin wa mahaifiyar ta magana kamar Fiyin.

Fiyin ta bata shawara ta zauna da mahaifiyar ta suyi abubuwa tare koda yaushe. A haka ne zasu fara neman darasin da zasu yi magana akai.

Fiyin ta gayyace abokan ta su ziyarta ta bayan makaranta. Bada jimawa ba, gidan Fiyi ya zama wajan haduwa.

Kin taba jin kamar ke daban ce da kowa kamar Fiyin? Muna son ki walwala ki zama kanki. Gaya mana abun daya banbanta ki a shafin sharhi.

Share your feedback