Wayyo! Bana son shugaban wajan aikin mu a Facebook dina!

Shafin ki, dokokin ki

Sannu Babban Yaya,
A kusan watani shida tun dana cika goma sha bakwai, bayan makaranta ina zuwa aiki a wani waje. A watan daya gabata na shiga Facebook. Ina duba sa a waya na a wajan aiki. Sai shugaban wajan aikin mu ya gan yace yana son mu zama abokai a facebook. Bai kamata muyi amfani da waya idan muna aiki ba, sai naji tsoro zan shiga matsala idan ban ce eh ba. Yanzu yana tura mun sakonnin sirri a Facebook, yana cewa mu hadu a wani waje. Yana hana ni sakewa. Me zan yi? Ina bukatan kudin domin na taimake kani na zuwa makaranta, kuma bana son nayi asarar aiki na, amma bana son abubuwan da yake fadi mun.

Nagode,
Ma’aikaciya mai damuwa


Sannu Ma’aikaciya mai damuwa,
Na fahimta cewa kina son ki goya bayan iyalin ki.

Amma ya nuna sarai cewa Oga ki na amfani da matsayin sa yayi amfani dake. Ya san cewa kina bukatan aikin nan. Bai kamata ba!

Mataki na farko da zaki dauka shine ki cire shi daga facebook dinki ko kuwa ki toshe shi daga shafin ki.

Idan kina jin tabbaci sosai, zaki iya gaya mishi cewa sakonnin sa na hana ki sakewa, kuma baki so.

Idan kina tsoron fuskance shi, kiyi wa wata/wani amintaccen babban mutum magana da zai taimake ki bi da al’amarin. Wannan zai iya zama wani a wajan aikin ku, ko mallamar ku a makaranta, ko kuwa wata abokiyar ki data girme ki sosai.

Idan wajan aikin ku nada sashen kula da ma’aikata, ki kai rahoto a wajan su.

Idan kina da wani dalili da zai hana ki shawo kan matsalar nan, kina bukatan yanke shawara ko zaki cigaba da aikin ko kuwa ki same wani aiki.

Ki tuna cewa ba laifin ki bane. Kada ki bawa kanki laifi!

Kina da dokan damar jin tsira a duke inda kike, harda wajan aikin ki.

Allah bada sa’a! Ina tare dake a zuciya.

Da kauna, Babban Yaya.

Share your feedback