A taimaka! Ban san yadda nake ji ba

Abun da zaku yi idan kuna son samari biyu

Sannu babban yaya,

Peter da Wale babban abokai na ne. Na san su tun da nake karama. Idan na shiga matsala, Peter na taimako na. Idan ina bakin ciki, Wale ke saka ni murmushi. Ina kaunar su sosai. Amma abubuwa sun canza. Duk sanda na ga Peter, zuciya na zai fara bugu. Ina jin wani iri a cikin jiki na. Ina ganin ina son abokantaka mu yafi haka. Amma zuciya ta na bugu idan naga Wale ma! Ina ganin ina son abokantakan mu yafi haka da shi ma.

Ban san wanda nafi so ba a cikin su biyu. Ban san nayi asarar babban abokai na biyu. Ban san abun yi ba, babban yaya ki taimaka!

Nagode,

Rikitacciyar budurwa

Sannu Springster!

Na farko, ke ba rikitacciyar budurwa bace. Ba abun dake damun ki. Idan muna girma, jikin mu da kuma shaukin mu na canzawa. Ba abun jin kunya ko tsoro bane. Dukkan mu mun taba samun kan mu a irin wannan al’amarin. Idan kina nan ke daya, wa kike tunani sosai– Peter ko Wale? Wa kika fi son kwashe lokaci da? Wannan zai taimake ki shawo kan matsalar, zai taimake ki sanin wanda kika fi so. Yana da muhimmanci ki kasance tare da mutumin dake son ki ma.

Saboda haka, ki saka ido a Wale da Peter. Suna nuna miki wani alama kamar suna son fiye da abokantaka? Wa ke bada uzuri sosai domin ya kwashe lokaci dake? Idan kika san gaskiya a zuciyar ki, zaki samu amsar ki.

Ki gwada kwashe lokaci dasu a cikin jama’a sosai. Zaki san safgar su da kuma burin su. Kuma zaki ga yadda suke bi dake a cikin jama’a. Bai kamata saurayin ki yaci zarafin ki ba. Ki tuna, ba komai bane idan baki kasance budurwar Peter ko Wale ba. Zaki iya canza ra’ayin ki idan kiga ga dama. Yin soyayya nada kyau, amma samun abokantaka yafi.

Ina fatan wannan ya taimaka. Allah bada sa’a.

Da kauna,

Babban yaya

Yawancin mu nada abokai maza. Abokantaka kawai ya hada mu, babu komai tsakanin mu. Hai sai mun ga cewa bamu son abokantaka kawai. Zai iya rikitar da mu, amma wadannan abubuwan nada hanyar aukuwa mana.

Kun taba son fiye da abokantaka da abokan ku maza? Gaya mana a nan kasa.

Share your feedback