Ya zan hana masu tsangwama a Facebook?

Zaku iya hana sharhuna mara kyau a shafin yanar gizo gizo

Sannu Babban Yaya,
Abokaina na saka jita-jita da gulmar yan ajin mu a shafin Facebook. Suna fadin abubuwa mara kyau. Ban tsammanin akwai gaskiya a cikin kowani daga cikin abubuwan nan ba. Bana jin dadin abun da suke yi. Amma ina tsoro zasu hau kaina idan nayi magana.

Me zan yi domin na hana su?

Da godiya,
Mai jin laifi


Sannu Mai jin laifi,
Abun da kike masaniya shine ake kira tsangwamar yanar gizo gizo. Shima yana da muni da rauni kamar tsangwamar da ake yi fuska da fuska. Saboda yana da lahani sosai, wasu kasashe suna na masa kallon laifi.

Kiyi kokarin yin wa abokan ki magana. Na san cewa zaki tsoratar yin musu magana, tunda ba ke suke yin wa tsangwamar ba. Kuma ba zan yi karya ba, wannan zai iya saka su juya suna tsangwamar ki ko kuwa su daina abokantaka dake! Amma dai kina son ki cigaba da abokantaka da masu tsangwama?

Hanya daya da zaki iya bi da wannan shina idan kika taimake abokan ki tunanin akan yadda zasu ji idan aka musu tsangwama.

Zaki iya cusa musu ra’ayi su daina ayyukan su mara kyau.

Idan bai auku ba, zaki iya taimakawa idan kika kai rahoton abun dake faruwa a wajan wata ko wani amintaccen babban mutum ko wajan mallamar ku. Mai yiwuwa kiyi asarar abokan ki, amma dai kinyi abu mai kyau.

Kuyi magana da wata ko wani babba ko wata babban abokiyar ki, ko yar dangin ku da kika yarda da, su taimake ki hana tsangwamar nan. Kuma zai iya tura sako cewa tsangwama bai da kyau.

Ki karfafa kanki!
Da kauna, Babban Yaya

Share your feedback