Ku karanta yadda Amira ta zama mai aikin sa kai
Suna na Amira. A matsayin budurwa, ina yawan tunani akan hanyoyi da zan taimake al’umma na. Ina son al’umma na ya kara inganta. Na san cewa dole wani yayi abu akan sa. Ni ce wannan mutumin.
Shiyasa na yanke shawara na zama mai aikin sa kai wa wani kungiya a al’ummar mu. Amma iyaye na basu goya mun baya ba, musamman mahaifina. Ya kira shi “wahala”. Yace zai janye mun hankali daga makaranta.
Suka ce na manta da aikin sa kai. Bani da wani ikon yin wani abu sai na yi biyayya. Nayi bakin ciki sosai. Amma na yanke shawara cewa bazan fidda rai ba.
Sai bayan dana kammala karatu na na jami’a, ina shirin bautan kasa (NYSC) na gabato mahifina.
Na gaya masa yadda bautan kasa na zai zama lokaci mai kyau da zan yi aikin sa kai. Na nema izinin sa domin na cimma burina. Abun ya bani mamaki daya amince.
Har ya bani shawara na samu aiki da wani kungiyar taimako mara riba da basu dogara da gwamnati (NGO). Ya kira wasu abokan sa su taimaka, kuma daya daga cikin su ya san wani waje dake kusa da inda aka tura ni. Sa’ar al’amarin shine, sun karbe ni.
Wannan ne farin tafiyana cikin bunkasar al’umma.
Bai zo da sauki ba da fari kamar yadda na zato. Na amince da mahaifina. Abun da wahala. Sanda na koya abubuwa da yawa a lokaci kadan.
Amma ban saka wadannan kalubalen su sanyaya gwiwa na ba. Na cigaba da maida hankali.
Kuma, ina son na nuna wa kai na cewa zan iya sarrafa masaniyar.
Koda yake akwai ranaku da naso na daina. Amma da goyon bayan mahaifiyata da wasu abokan aiki na iya bi da wahalar.
Masaniyar ya bude mun ido sosai. Na koya sabobin abubuwa kamar yadda ake amfani da kwamfuta. Har na koya yadda zan yi magana a cikin jama’a; wannan ya taimake ni gina tabbaci na.
Mafi muhimmancin, na koya cewa zan iya yin kowane abu mutakan dai na yi kwazo kuma ina so.
Shekaru da yawa sun wuce dana yi aikin sa kai a al’ummar nan amma nayi amfani da masaniyar na cimma abubuwa da yawa.
Kuna nan kamar Amira? Akwai wani abu da kuke so sosai? Kuyi aiki sosai domin ku cimma burin ku. Kalubale zasu iya zuwa, al’ada ce. Ku tsaya da karfi.
Kuma kamar Amira, idan iyayen ku basu goya bayan ku ba, ba komai. Ku gwada yin musu magana. Ku bincika dalilin daya sa basu goyo bayan burin ku. Ku bincika abun da suke so kuyi a maimako. Ku fara yin sa. A lokaci kadan mai yiwuwa biyayyan ku zai biya.
Wani abu da zaku iya yi kuma shine yin wa wata ko wani babban mutum magana, kamar Inna/Kawu/Kakanin ku/ ko kuwa wani da iyayen ku ke girmama. Ku tambaye su suyi wa iyayen ku magana.
Menene abun nan da kuke son yi sosai? Me kuke yi akan sa ko kuwa me ke hana ku bin sa? Ku rarraba da mu a sashin sharhi.
Share your feedback