Yadda na koya kasuwancin daga mahaifiyata

Beyi lati ba ki koyi wani sana'a

Yawancin abokai na suna gaya mun yadda suke barci da lati sosai a karshen mako. Ama ni kam babu banbanci tsakanin ranar mako da karshen mako saboda mahaifiyata na tada ni da wuri kowana rana na taimake ta da aikin gida tare da tsaftace wajen yin gashin ta.

Sunana Bimbo kuma shekaru na goma sha biyar. Nice babba a cikin yara a iyalai biyar. Ina da yan uwa uku maza da kuma ‘yar uwa guda daya kuma dukan mu mahaifiyar mu ta duba mu. Mahaifi na a rasu shekaran daya gabata shi yasa muka tsira daga kudin da mahaifiyata ke samu daga sana’an wajen yin gashinta.

Mahaifiyata nada customomi sosai kuma wasu lokutan bata iya jurewa da yawar lamban su musaman a karshen mako. Ina taimaka mata, da kwance gashi, da wanke gashin customomin ta. A wasu lokutan ina marmarin zuwa waje nayi wasa da abokane na ko kuma da kanne na a maimakon zama a shagon mahaifiyata.

Mahaifiyata tace tana shirya mun zaman gaba mafi inganci shiyasa take koya mun “yadda zan kamo kifi da kaina” tun da wuri. Tace da irin wannan kwarewa zan fara hada kudi na kaina dawuri kuma mai yiwuwa ba sai naje neman aiki idan na kammala makaranta.

Kuma mahaifiyata nada gaskiya soboda a wasu lokutan ina taimakan abokai na da yan ajin mu yin kitso a makaranta a saboda ana dukan su a makaranta dan rashin yin kitso. Ina ajiye kudade da nake samu saboda ina son na siya wani yadi dana gani a talabijin. A lokacin hutu zan ta aiki dan na samo kudi.

Wasu abokane na cewa dama sune ke da kwarewa saboda amfani su samu Karin kudi. Wasun su sunce zasu yi wa iyayen su Magana su yarda su koya yadda ake kitso lokacin hutu Ina godiya da mahaifita. Nasan watarana zan yi amfani da wannan kwarewan na goyo bayan ta da kanne na.

Kina da wani abu mai matsananci da kike so? Kina son ki taimaka kanki da kuma iyalin ki? Ki koya wani sabon abu mai mahinmanci yau mana!

Share your feedback