Yadda na fara kasuwanci da kudin aljihu na

Kasuwancin siyar da kati na Lateefat

Tunanin ku (4)

Mahaifina ya rasu da nake shekaru goma sha hudu. Mahaifiyata ta kasa lura da ni da yar uwa ta.

Da nake shekaru goma sha biyar, ta tura ni zama da dan uwan ta.

A wajan sa ne na fara kasuwanci na na farko.

Kun gani, dan uwan mahaifiya ta na bani naira dari na kudin aljihu kowane rana. Na yanke shawara na fara ajiye naira hamsin daga ciki.

Bayan wata biyu nayi ajiyan dubu uku. Nayi tunanin abun da zan yi da kudin.

Nayi magana da dan uwan mahaifiya ta akan ajiya na. Ya bani shawara na fara kasuwancin siyar da katin waya dashi.

Ya kai ni wajan wani dillali daya saida mun katin dubu biyu da dari biyar.

Na fara da siyar da katin wa dan uwan mahaifiya ta da kuma makwafta mu. Sai na gaya wa abokai na da iyalai su akan sana’a na.

Na fara siyar wa wasu mutane a titi. Domin na tsirata kai na, dan uwan mahaifiya ta ya tambaye abokiyar sa ta barni na zauna a gaban shagon ta na siyar da kati na. Ta nan, wani zai san inda nake da wanda nake magana da a kowane lokaci.

Sana’a a samar titi zai iya jawo hatsari, na tsirata kaina ta tabbata cewa bana nan ni daya kuma idan ina magana da abokan sana’a na, bana barin maganar ya wuce gona da iri kuma bana taba bada bayanai na masu amfani kamar lambar waya ko kuwa adireshi na koda lokacin da wasu maza suka tambaye ni wannan.

Kuma dai na siyar da kati a coci kuma na siyar wa wasu mallamai da dalibai a makarantar mu sai nayi amfani da wannan darasin da dan uwan mahaifiyta ya koya mun na tsirata kaina.

Bayan watani shida na ajiye dubu biyar daga kasuwanci na.

Ina ta murna. Ban taba tsamanin cewa zan iya samun kudi da yawa haka ba. Yanzu ya kai shekara daya dana fara kasuwancin siyar da kati na.

Nayi kokarin taimakon mahaifiya ta. Kuma nayi kokari na ajiya kudi na rayuwana na gaba.

Kema zaki iya farawa yau. Baki bukatan samun kudi da yawa, ki fara da abun da kike da.

Kina samun kudin aljihu daga iyayen ki ko kuwa wani mai tsaran lafiyan ki? Kiyi ajiya daga cikin sa.

Kina samun kudin aljihu daga iyayen ki ko mai tsaran lafiyar ki? Kiyi ajiya daga ciki.

Baki samun kudin alijuhu? Akwai sauran hanyoyi.

Kina da wani kwarewa ko lokacin koyon wani kwarewa kamar gyaran kayan gida, ko yin kitso, ko yin dutsen ado, ko kuwa yin fenti. Abokan arziki, ko yan ajin ku da kuma iyalin ki zasu iya biyan ki kiyi amfani da wannan kwarewar ki taimake su.

Akwai sauran hanyoyi masu tsira da zaki samu kudi. Ga misali, zaki iya sa kai ki kai sako wa makwafta, ki taimake su wanke motar su ko kuwa kayan su domin su biya ki. Duk shawarar da kika yanka, ki tabbata kin saka wani yasan wajan da kike a kowane lokaci.

Kema zaki iya zama karamar mace mai kasuwanci. Duk yana daukan horaswa da aiki sosai.

Kina ajiyen kudi? Meyasa kike aijya? Kin taba tunanin akan fara kasuwanci? Gaya mana akan sa a wajan sharhi.

Share your feedback

Tunanin ku

ina tayaki murna hakan

March 20, 2022, 8 p.m.

Test - anonymous comment

March 20, 2022, 7:58 p.m.

Latest Reply

Test - anonymous reply

Test - normal comment

March 20, 2022, 7:58 p.m.