Yadda na fara kasuwancina na farko

Abun da tsoro amma Biola tayi nasara

Shekaru na goma sha shida dana yanke shawarar fara kasuwancina na farko. Ina son abun da zai kawo mun kudi. Ina son na iya lura da kai na amma bani da kudi.

Na yanke shawarar fara kasuwancin alkaki da tuwan madara saboda na san cewa yaran unguwan mu zasu siya.

Fara kasuwanci na bai zo da sauki ba. Bani da kudin farawa. Amma ban saka wannan ya hana ni ba.

Wata rana nayi wa kawu na magana. Na gaya masa akan ra’ayin kasuwanci na kuma ya yarda ya bani kudin da zan fara.

Wannan ne alamar fara tafiyar zaman mai kasuwanci. Tafiya ne mai kyau saboda na fara samun riba da sauri.


Na samu na siya wasu kayan ado da nake so. Har na iya biyan wasu bukatu na.

Gaskiyar shine kasuwancin ya taimake rayuwana.

Shekaru biyar sun wuce tun dana fara kasuwancin kuma ina godiya cewa zan iya biyan wasu bukatu na. Bana dogara da kowa.

Yanzu ba sai na roke kowa kudi ba a maimako, yanzu ina taimakon mutane da kudin dana samu. Ina da aikin yi.

Shawara na wa matasa shine ku samu wani abu da zaku iya yi sai kuyi sa. Ba sai kun dogara da kowa ba. Dukkan mu zamu iya cin nasara. Eh na san idan muka fara zai iya yin wuya amma idan kuka cigaba yin sa abubuwa zasu fito da kyau.

Kuma kada kuji tsoron tambayen taimako. Idan akwai wata ko wani amintaccen babba da zai iya taimakon ku, kuyi musu magana. Amma ku kula dai. Wasu mutane zasu iya amfani daku, baza ku iya yarda da kowane mutum ba.

Kun fara wani kasuwanci? Fada mana yadda kuka yi sa a sashin sharhi.

Ku karanta wannan makalar domin ku koya yadda zaku fara da kuma yadda zaku bi da kasuwancin ku

Share your feedback