Yadda na juya lokacin da bana komai zuwa wata hanyar samun riba

Yadda Asma’u ta samu riba da kwarewar ta

Ina yawan kwashe lokacin da bana komai ina labari da abokai na, ko na ta waka ni daya ko kuwa na ta wasa da kanwa ta.

Wata rana nayi wani wasa da abokai na akan fara kungiyar waka. Da farko, suka mun dariya. Sai suka ga cewa da gaske nake. Sai wasun su suka yarda suka hade da ni.

Mun yanke shawara mu amfani da ranaku guda biyu a sati dan mu gwajin kwarewar mu, sai muka tsara cewa zamuyi waka a gaban gidan mu ko wane maraicen asabar domin mu nishadantar mutane masu wucewa.

Wata rana, muka lura cewa yaran farfajiyar mu suna sauraren mu idan muna gwajin kwarewar wasu wakokin mu. Suna mana tafi idan muka gama.

Bada jimawa ba wasu manyan mutane suka fara luran mu. Aunty Hauwa da take cikin masu kallon mu tace mu zo muyi musu waka da abokan ta. Da muka gama suke ta mana tafi. Har suka bamu kudi.

Daga nan,Mrs Madu, wata mallama a cibiyar asibitin lafiya a al’ummar mu ta gayace mu muzo muyi musu waka.

Da muka yi musu waka, naga yadda mara lafiyan nata jin dadi da muka yi wakan da yaren mu. Basu so mu tsaya ba.

Yanzu haka yawancin yan mata a ungwan mu nason su hade da kungiyar wakan mu. Har naji wasu samarai ma sun hada nasu kungiyar waka.

Nayi sabobin abokai daga kungiyar waka na. Muna nan kamar yan uwa daya a kungiyar. Ta kungiyar munyi kokari mun taimakon juna da wasu matsalolin mu a gida da kuma makaranta.

Ina murna domin na taimaka nasa mutane murmushi a lokacin sukuni na.

Kiyi amfani da roguwan lokacin da bakia komai da wayo. ki koya wani sabon abu, ko kuwa kiyi aiki akan kwarewar ki. Ko ki zama kamar Asma’u ki fara wani kungiyar ko mai yiwuwa wani kungiyar karatu, ko kungiyar dinki ko kuwa kungiyar rawa.

Gaya mana a shafin sharhin mu yadda kika kwashe lokaci a lokacin sukunin ki.

Share your feedback