Abokai guda nawa ya kamata na samu?

Titi ta zabi inganci a maimakon yawan abu

A makarantan mu, shigan wani kungiya shine abun yayi. Idan baku wani kungiya, toh baku hadu ba. Karshen zance.

Mutane da yawa suna yin abubuwa da basu son yi. Duk saboda suna son su zama daya daga cikin yaran da suka hadu. Wasu ma har suka fara kwashe lokaci da mutanen da basu so. Kawai don suna son su nuna cewa suna da abokai da yawa. Abun da hauka.

Sai nayi bincike na lura cewa abokantaka ba akan samun yawan abokai bane, amma samun abokai masu inganci. Na fara maida hankali a irin abokan da nake da a maimakon yawan su. Me dalilin samun abokai goma idan babu wanda ke goyon bayan ka? Ko kuwa basu nan a lokacin da kuke bukatan su sosai? Eh, muna fuskanta matsin lamba sosai muyi abun yayi. Amma kasancewa asalin kanku yafi. Idan kuka yi imani da asalin kanku, zaku samu abokan alheri da zasu yi kaunar ku a yadda kuke. Kamar abokiyata guda, Jamila. Tana goya mun baya a kowane lokaci da nake bukatan ta. Tana taimako na da kowane irin abu. Muna kula da juna a cikin kowane al’amari.

Muna karanta labaran Springster tare. Har tana siyo mun yan kananan abubuwa a kasuwa. Kuma abu mafi dadin? Ba sai tana neman abu bane take kira na. Ko kuwa ta mun gori. Zata iya kira na muyi magana akan abun da taci da safe! Toh asalin abokantaka kenan.

Mun san komai game da juna. Bata hukunta ni. A taikace dai, ta fahimce ni. Ba zan musayar ta ba wa karin abokai. Abokiya ce miliyan a cikin daya. Nayi murnar samun ta a rayuwa na. Ina fatan kuma zaku samu naku Jamila da wuri.

Kuna da wasu abokan kwarai? Menena wani abun musamman game da su? Ku rarraba da mu a nan kasa.

Share your feedback