Yadda mahaifiyata ta taimake ni yakin miyagun kwayoyi

Yanzu ina da lafiya kuma na warware

Idaya ta rarraba da mu labarin ta akan yadda ta samu damar yakin miyagun kwayoyi. Ku karanta ku koya.

A shekaru hudu da suka wuce na hadu da wasu sabobin kungiyar abokai. Ina makarantar sakandare a lokacin.

Ina budurwa kuma babu isasshen wayo. Wadannan kungiyar abokan nada tasiri akai na sosai. Sun gabatar dani a shan kwayoyi kuma ban yi tunanin hatsarin sa ba.

Ban san abun da sakamakon zai mun ba. Na zata babu komai domin kwayoyi ne kawai.

Nayi tunanin kawai zan sha su ne nayi bacci. Na fara daukan su kafan na sani na shaku dasu.

Da mahaifiyata ta sanni tayi bakin ciki. Dole ta canza mun makaranta. Ta fara kula da ayuka na kuma ta tabbata cewa ta raba ni da wadannan abokan da suka koya mun shan kwayoyi.

Da taimakon mahaifiyata nayi kokarin daina shan kwayoyi. Bai zo da sauki ba. Sanda nayi fama da ciwon janyewar. Nayi wahala sosai har nayi tunanin koma shan kwayoyin. Amma na san cewa wannan ba ra’ayi bane. Na san mahaifiyata zata yi fushi dani kuma zata mun dukka idan na sake shan kwayoyi. Naji tsoron kasada da kuma sakamako dake zuwa da shan kwayoyi.

Mahaifiyata ta shawarta ni a dukkan wannan lokacin.

Ta gaya mun zan iya yakin miyagun kwayoyin nan. Tace zai iya hana ni inganta rayuwa na. Tace idan ina son rayuwata na gaba yayi kyau, na guje kwayoyi.

Ya kai shekaru hudu tun da wannan ya faru. Na canza abokai na. Ina kula da irin mutanen da nake abokantaka da. Yanzu na kara samun tabbaci. Mutane baza su iya tasiri ni ba.

Bana bukatan kwayoyi domin nayi aiki.

Ina farin ciki sosai saboda na iya dainawa domin lafiyar jiki na, da kwakwalwa na, da kuma rayuwata na gaba.

Shawara na muku shine ku zabi abokan ku da wayo. Kada ku bari wani ya tasiri ku in ba dai akan abu mai kyau bane. Kuyi tabbaci da kanku. Ku guje kwayoyi.

Share your feedback