Taga wata dama kuma ta kama shi da hannun ta biyu
Wasu lokuta zai iya yi kamar wanda suka girme ku basu gane ku ba da kuma bukatun rayuwar zamani. Amma za’a iya samun hikima a masaniyar su.
Labarin Portia ya nuna mana yadda yake.
Surukar tace ta jagoranci ta zuwa sana’ar ta na fari. Bayan data haife yar ta na farko, tana neman abun da zai taimaka da zanen haihuwar ta. Dukka abubuwan data yi amfani da, basu yi mata aiki ba. Sai surakarta ta bata shawara tayi amfani da marula oil. Wani mai ne da ake samuwa daga wani sanannen ‘ya’yan itatuwa da ake samuwa a sashin kudu da kuma yammaci a nahiyar Africa.
Portia ta gwada amfani dashi kuma tayi mamakin sakamakon. Yayi mata aiki fiye da dukka sauran abubuwan da tayi amfani da. Ta rarraba a facebook yadda ya gyara mata fatan jiki da kuma kamanin zanen haihuwar. Abokan ta nata bada sharhuna masu kyau, musamman sanda suka fara tambaya inda zasu iya samun man nan.
A nan ne Portia ta fara aiki tana binciken abun musamman game da man. Ta fara tattara a kwalba daga madafar ta tana siyar wa abokan ta. Domin suna son sa sosai, suka siya da yawa.
Portia ta san cewa karamar sana’a ne kuma ba zai bata kudin da take so ba. Ta samu shawara daga kawun ta dake aiki a wani masana’anta. Tana son ta hada da wani man shafawa, domin ta siyar a kantina. Amma kafan ta siyar dasu, sai ta sa anyi gwajin su kuma an amince dasu a wajan hukumar masana’anta.
Portia ta tura samfurorin ta zuwa hukumar masana’antar kuma ta samu amsar ta take so. Bayan da ta kwankwasa kofofin mutane da yawa, wani shagon siyar da kayan sari suka yarda su siyar da kayan ta. Abubuwa sun kasance da kyau wa Portia yanzu da har tana son ta fadada kasuwanci ta zuwa man gashi.
Menene wani abun mamaki daya albarkace ku da kuka koya daga wasu da suka girme ku? Ku rarraba damu a sashin sharhin.
Share your feedback