Ina kunyar yin wa Inna na magana

Simi ta koya yadda zata fadi abun dake ran ta

A yan watanin da suka wuce na dan yi bakin ciki. Munin al’amarin ma shine bani da kowa da zan iya yin wa magana akan matsaloli na.

Bai dade da muka dawo jihar Lagos da Inna na ba. Saboda haka bani da abokai. Ina kwashe yawancin lokuta na tsakanin taimakon Inna na a shagon ta da kuma makarantar horar kwamfuta.

Ina zaman kadaici. Ina kasa yin wa Inna na magana.

Mutum daya ne kawai zan iya kira aboki, shine wani Michael mai shekaru ishirin dake makarantar kwamfuta da nake zuwa.

Mun zama abokai da sauri.

Ina son sa sosai har ina marmari dama ya zama saurayi na koda ya bani shekaru uku. Amma ban san yadda zan gaya masa ba.

Babu kowa kusa da zai bani shawara akan abun da zanyi da yadda nake ji. Inna na ba ra’ayi bane. Bana son tayi mun dariya. Ko kuwa ta fadi abubuwa kamar “Simi na sha’awar wani” ko kuwa ta kira ni “ Mai soyayya”.

Sai wata rana bayan ajin mu na gaya wa Michael yadda nake ji. Yayi mamaki. Ya ce mun yana kallo na kamar kanwar sa. Yace yana son mu zama abokai ne kawai. Abun ya saka ni bakin ciki. Inna na ta lura. Ta tambaye ni abun dake damu na.

Ban san yadda zan gaya mata ba. Tayi barazanan duka na idan ban yi magana ba.

Na gaya mata abun daya faru.

Abun ya ban mamaki cewa bata yi mun dariya ba. Ta tambaye ni mai yasa ban zo na same ta tun da farko ba. Na gaya mata ina kunya ne kuma bana son tayi mun tsiya.

Tace baza ta taba mun dariyar abun daya shafe zuciya ba. Tace ta taba samun kanta a irin wannan al’amarin.

Ta gaya mun abun da nake ganin na al’ada ce. Ta ce mun kada na bari martanin Michael ya dame ni.

Ina ji dama nayi mata magana kafan na kusanto Michael.

Shawara na shine, ku koya yadda zaku fadi abun dake ran ku. Kada ku taba jin kunya ko kuwa tsoron tambayen taimako. Ku nemo wata amintaccen babba mace da zaku yi wa magana.

Ku samu lokaci daya dace da zaku yi musu magana misali, zaku iya fara wani magana idan kuna kallon talabijjan ko kuwa kuna abinci tare.

Kuma idan kuna jin tsoro ko kuwa kunyar fara yin musu magana, zaku iya yin gwajin abun da kuke son kuyi musu magana a gaban madubi da wata abokiyra ku. Idan kuka yanke shawara yin wa wata babba magana kuyi tunanin kamar kuna yin wa wata abokiyar ku magana. Zai rage tsoron da kuke ji idan kuna musu magana.

Gaskiyar shine idan kuna da amintaccen babba mutum dake jagorar daku, baza ku samu daman kuskure ba.

Da kuna matsayin Simi me zaku yi dabam? Ku rarraba amsar ku damu a wajan yin sharhi.

Share your feedback