Seyi ta bada labari ta akan yaron da take so
Suna na Seyi kuma shekaru na goma sha hudu. A makonnin da suka wuce na ga wani yaro yana tsayiwa da wasu samari a ungwan mu. Yana da kyau da tsayi.
Ranar dana fara ganin sa kenan.
Ina ta kunya dana gan su. Ina ganin ma nayi i’ina da daya daga cikin su dana sani ya kira suna na ya gaishe ni.
Dayan ranar ya ziyarta dan uwa na a gida. Na binciko cewa sunan sa Kunle kuma abokin dan uwa ne. Daya gaishe ni ina ta kunya ban san yadda zan amsa shi ba.
Kwanan nan, ina ta ganin Kunle sosai da yake yana yawan kwashe lokaci da dan uwa na. Ina jin tsoron yin masa magana.
Na gaya wa yar uwa ta akan sa kuma na tambaye ta akan abun da zan iya yi.
Ta mun dariya da taga ina karkarwa sai tace
“Seyi abun da kike ji abu ne da aka saba da. Kina sha’awar sa ne. Wannan yana nufin cewa kina son sa. Babu komai da wannan.
Duk da haka, abun da zaki yi da sha’awar shine mafi muhimmanci.
Yawancin lokuta yana daukan fiye da sha’awa domin ki gina dangantaka da wanda kike so.
Kina bukatan daukan wasu matakai domin ki gina abokantakar.
Zaki iya farawa ta gabatar da kanki ma sa. Ki same shi kawai ki ce sannu, suna na Seyi.
Kiga yadda zai amsa. Kada ki damu idan bai miki fara’a ba.
Akwai lokuta da muna son mutane amma su basu son mu.
A lokuta kamar haka ba amfanin jin bakin ciki. Zaki samu wani dake son ki kamar yadda kike son sa.
Amma idan ya amsa ki da kyau, kada ya dauke hankalin ki. Ki gwada gina abokantaka na gaske da shi tukun.
KI binciko idan yana son ki ko baya yi. Zaki iya yin wannan ta lura da halayyar sa. Kamar ko yana da kunya ko jin tsoro idan yana kusa dake? Yana son magana dake a waya ne , ko fuska da fuska, ko kuwa a shafin sada zumunta? Kada kiyi ko wani abu da gaggawa. Zaki ci nasara.
Hankali na ya kwanta bayan da nayi magana da yar uwa ta. Na tsara cewa zan yi dukkan abubuwann da ta fadi a mako na gaba idan Kunle yazo ganin dan uwa na.
Sannu yan Springster, son wani yaro ba laifi bane. Abun da kuka yi akan sa ne mafi muhimmanci.
Kuna al’amari daya da Seyi? Ku bi shawarar yar uwar Seyi ko kuwa kuyi magana da wani amintaccen babban mutum.
Share your feedback