Na tura wa wani yaro hotuna na

Ina ji dama ban yi ba

Abokantaka na da Peter ya jima sosai. Kowane dare muna magana a waya, wasu lokuta zamu yi magana da dadewa.

A makonni kadan da suka wuce, ya tambaye ni na tura masa hotuna na tsirara. Nayi dariya da farko sai na gaya masa “Ba zai faru ba!” Ya fara tura mun sakonni yana roko na na tura masa daya. Na share shi, ina fatan zai daina.

Wata rana, da muke hanyar zuwa gida yace muyi gasar tsere. Yace wanda bai ci gasar ba zai tura wa wanda yaci nasara hoton sa a tsirarar. Na yarda. Ko ta ya dai - Ban ci nasara ba.

Na tura masa hoton na da rigar mama. Ya roke ni na cire rigar maman - yace yana bi na bashi. A karshe na yarda na tura masa hoto na tsirara.

Nan take nayi bakin ciki. Na ce masa ya goge shi, sai yaki. Na rikice. Ina bakin ciki. Na zata abokina ne.

Nayi kunyar ayyuka na. Na fara boye abubuwa a zuciyata. Mahaifiyata ta lura canji a hali na. Tayi kokari ta bincika matsalar. Duk da haka, naji tsoron gaya mata abun daya faru. Bana son na bata mata rai.

Amma na san dole lokaci zai kai da zanyi magana. Bana son na boye mata komai. Kuma, bana son na karya alkawari dana yi na riga zuwa wajan ta koda yaushe idan ina da matsala.

Na san zan iya yarda da ita koda tana dan fushi.

Saboda haka, sai na same ta. Na roke ta ta bi dani da hankali. Na san nayi kuskure. Ta yarda. Dana gaya mata abun daya faru tayi mamaki kuma taji kunya. Amma sai ta bi dani da hankali kamar yadda tayi alkawari.

Tace mun, idan yan mata na yin girma kuma suna masaniyar balaga, mai yiwuwa su fara jan hankalin samari. Wasu lokuta, wadannan samarin ko kuwa abokai zasu iya matsanta musu su gwada yin abubuwa da ke hana su sakewa. Saboda kowa nayi. Amma a lokuta irin haka, yana da muhimmanci muyi magana da mutane da zamu iya yarda da, su bamu shawarar daya dace. Mutane kamar iyaye, masi tsaran lafiyar ku, ko kuwa wata abokiyar ku.

Tare, muka tattauna ra’ayoyin yadda zamu shawo kan wannan al’amarin.

A karshe, muka yanke shawara muyi wa Peter magana tare. Ta koya mun yadda zan gaya mishi cewa na rikice kuma ina fushi dashi. Wannan ya taimake Peter gane cewa ayyukan sa sun raunata ni kuma wannan ya saka shi goge hotunan.

Na ji dama nayi wa mahaifiyata magana da sauri - Babu wani matsala da baza ta iya shawo kan sa ba.

Yan mata muna son ku san cewa;

  • Tura hotuna dake hana ku sukuni baya cika kasancewa da kyau. Zai iya shiga hannun wani da bai kamata ba.
  • Mutane dake matsanta muku ku tura hotunan ku dake hana ku sukuni na iya kasancewa da nufi mara kyau.
  • Koda mahaifiyar ku ce, ko yar uwar ku, ko abokan ku, ko kuwa makwaftar ku - ku nemo wani da zaku iya kai wa rahoto ko kuwa kuyi wa magana.

Kun taba yin wani abu da baku yi alfahari da a cikin matsi? Ku gaya mana yadda kuka bi da al’amarin bayan daya faru a sashin sharhi.

Share your feedback