Ni Sananniya ce

Amma bani da hali mai kyau

Suna na Elizabeth. Shekaru na goma sha biyar, kuma ina zama a Lagos. Ina da abokai da yawa amma idan na kala baya na lura cewa sun saka ni yin abubuwa da bana alfahari da.

A tsohon ungwan mu ina cikin wani kungiyar babban yan mata. Mune hadaddun yan matan ungwan mu.

Yan matan kungiyar basu damuwa da kowane mutum sai kansu. Basu goyon baya na. Suna karfafa ni nayi abubuwa da basu da kyau. Suna dariya idan na raina iyaye na. Suna ganin wannan nada kyau.

Bana son nayi asarar abokantakar su sai na wayance kamar wannan halin nada kyau.

Zamu tsokane yan mata a ungwan mu kuma muyi dariyan kayan su ko kamanin su.

Wata rana iyaye na suka gaya mun cewa zamu koma wani waje. Nayi bakin ciki. Ina kewan abokai na kafan ma mu tafi. Ban san abun da zanyi ba tare da kungiya na ba.

Na sami kaina a wani sabon ungwa. Ya cika da sabobin mutane. Bani bane hadaddiyar yarinya kuma. Nice sabuwar yariya mara abokai. Wanda wasu mutane ke yin wa dariya.

Amma sai na hadu da Mary. Ta san bambancin akan abu mai kyau da mara kyau. Tana goyon baya na duk sanda wani ya tsokane ni. Ta karbe ni da hanu biyu.

Ta koya mun akan kasancewa mutum da hali mai kyau. Na fahimta yanzu cewa halayye na na da basu da kyau.

Na koya bi da mutane da kyau. Bana tsokanan sauran yan mata. Kuma na koya daina bin mutane saboda ina son na zama sananniya ko kuwa a so ni.

Yakamata dukkan mu mu kasance kamar Mary ko kuwa mu samu abokai kamar Mary.

Abokai masu kyau da zasu koya mana yadda zamu nuna halayye masu kyau da kuma karfafa mu mu kara inganta rayuwar mu.

Akwai wata kamar Elizabeth kusa daku? Ya kuke tunanin zaku iya taimakon mutane kamar haka canzawa? Kuyi mana magana akan sa a sashin sharhi.

Share your feedback