Idan na kasance shugabar kasa

Dupe tayi rubutu akan muradin ta

Suna na Dupe. Shekaru na goma sha shida.

Buri na shine na zama farkon shugabar kasa mace a Najeriya.

Idan na zama shugabar kasa, zan canza abubuwa da yawa.

Za’a samu makarantu masu kyau da kuma ilmi a kyauta.

Za’a kashe auren yara!!

Makarantar jama’u zasu samu motocin zuwa makaranta.

Asibitoci zasu lura da mutane a kyauta. Likitoci baza su taba zuwa yajin aiki ba.

Kasar zai kara samun tsaro. Zan tabbata cewa yan sanda sun samu horaswa da kyau.

Za’a hunkuntar azzaluman shugabanni.

Za’a samu karin aiki. Ma’aikata baza suyi zanga-zanga kafan a biya su ba.

Za’a riga biyan wanda suka yi murabus da wuri.

Surufi zai kara arha.

Najeriya baza ta dogara da kudin mai kawai ba. Zan naima wasu hanyoyi. Zan zuba jari a wasu albarkatun kasa.

Rikicin addini zai kare. Na san yana ji kamar a wani lokaci mai nesa ne. Amma na fara aiki zuwa zaman shugaban kasa.

Ina sane da abubuwan dake faruwa a al’umma. Ina sa kai wasu lokuta a cibiyar al’ummar mu.

Na dauka matakin matsayin shugabanci a wani kungiyar rawa dana hada.

Zamu iya zama duk abunda muka saka ran mu a ciki. Yana farawa da imani da muradin mu. Sai aiki domin mu ci nasara.

Idan kika zama shugaban kasar Najeriya, me zaki yi? Gaya mana a shafin sharhi.

Share your feedback