Idan zaku iya tunanin sa, zaku iya yin sa

Yasmin ta nuna mana yadda ake yin sa

Koda yaushe ina son gyaran abubuwa. Ko sanda nake karamar yarinya, zan hau kujera na canza kwan lantarki, ko kuwa na gyara wani sauya.

Iyaye na basu san abun yi da ni ba. Ban kasance kamar ‘yar da suke fatan ba. Amma sun ga yadda na kware, sai suka kyale ni. A karshen makonni, suna kai ni wani shagon mai gyaran kayan lantarki domin na kara koya.

Da nake shekaru goma sha daya, wani abu ya faru. A tsakar ranar lahadi. Iyaye na na kallon wani wasan kwakwaiyo da suke so sai kawai! Talabijin din mu ya kone! Suka fara fargaba suna ihu kamar anyi rasuwa.

Na kasa jurewa naga iyayena na fargaba. Nayi kokari na cusa musu ra’ayi su bari na gyara talabijin din, kuma suka yarda. A wannan lokacin, zasu iya amince da kowane abu. Suna fargaba.

Dana kwance talabijin din, zuciyana ya fara bugu. Sai na kwantar da hankalina na tuna komai dana koya daga shagon mai gyaran kayan lantarki. Na bi matakan, na kunna talabijin din sai ya fara aiki!

Iyaye na suka yi murna suka rarraba labarin da makwaftan mu. Kafan na sani, na zama zakaran al’ummar mu. Mutane suka fara biya na kudi na gyara musu abubuwa. Daga rediyo zuwa abun kallon bidiyo, dukka ina gyara. Har na hada wani karamin agogon kararrawa.

Bada jimawaba iyaye na suka daina bani kudun aljihu. A maimako, na fara taimako da siyan kananan kayan gida. Dana gaya musu cewa ina son na karatan darasin injiniya, iyaye na suka yi alfahari da ni. Yar su zata zama farkon mace ta zama injinya a al’ummar mu!

Amma wasu masu bakin ciki suna fadin cewa aikin injiniya ba aikin mace bane. Suka ce na zama wanzamiya ko kuwa tela a maimako. Wani mutum ma yace ba zan samu miji ba- kamar nace masa ina nema wani ne. Amma duk da haka, nayi bakin ciki. Kawai ina son nayi abun da nake so.

Iyaye na suka ce kada na damu. Suka ce idan mutane suka ga muna cin nasara, zasu so su jawo mu kasa. Suka karfafa ni na maida hankalina a aiki na kuma na watsi da masu bakin ciki. Wannan ya saka hankalina ya kwanta.

A yau ina kan gyara abubuwa wa yan al’ummar mu. Kuma ina aiki sosai domin na zama injiniya. Ba abun da zai hana ni. Idan zan iya tunanin sa, zan iya yin sa.

* Kamar Yasmin, ku ma kuna da naku basira na halitta. Babu wani abu mara kyau a cikin samun aikin yi a rayuwa na gaba. Kada ku bari kowa ko wani abu ya hana ku cimma burin ku. Menene wannan abun da kuka iya yi? Ku ajiye wani sharhi a nan kasa.

Share your feedback