Yana da kyau mace ta gaya wa namiji tana son sa?

Fadin abun dake zuciyar ku nada kyau

Sannu Babban Yaya,

Akwai wani yaro a al’ummar mu da nake so. Abokina ne. Na dade da sanin sa. Ina son mu zama fiye da abokai dashi. Bai ce yana so na ba kuma bana son wannan damar ya wuce ni. Abokai na sunce ba al’adar mace bane ta gaya wa namiji tana son sa. Sunce wajibin maza ne su gaya wa yan mata suna son su. Sunce zai rage mun daraja.

Yanzu ban san abun yi ba. Yana da kyau na gaya masa ina son sa? Ina fatan jin daga wajan ki.

Nagode
Helen.


Sannu Helen,

Gaskiya babu amsa kai tsaye wa wannan tambayen.

Muna wani bangaren duniya da ake ganin wajibin namiji ne ya gaya wa yarinya yana son ta. Kuma saboda haka idan mace ta gaya wa namiji tana son sa ana ganin ta kamar bata da da’a. Saboda haka wannan zai iya bawa yan maza mamaki idan mace ta gaya musu cewa tana son su.

Amma wadannan ra’ayin na canzawa kuma wasu yan maza na ganin kansu daidai da mata kuma maiyiwuwa amsar sa zai banbanta da abun da kika saba. Akwai kuma wani ra’ayi cewa zai yarda. Mai yiwuwa ya ganki kamar wata mai tabbaci. Yarinyar da ta san abun da take so. Wannan zai iya saka shi sha’awar ki.

Irin wannan yaron ne ya kamata ki ajiye, duk da yake suna da wuyan gani. Ya zaki same shi? Ki duba alamu ko yana son mace mai tabbaci da kuma nata ra’ayin, kuma yana girmama ra’ayin ki.

Idan yana da yaranta zai yi miki dariya domin kin ce kina son sa, ko kuwa ya gaya wa sauran mutane...Idan shi irin wannan yaron ne, toh gaskiya zai fi ki share shi. Mai yiwuwa kiyi bakin ciki da farko, amma ki tambaye kanki dalilin daya sa zaki so ki fita da wanda baya girmama ki.

A karshe, komai ya dangana da ke idan kina son kiyi amfani da wannan damar.

Kuma kafan ki dauki matakin shigan wani soyayya ki tambaye kanki wasu tambayoyi na gaske kamar, na shirya wa yin soyayya? Ina da karfin halin gaya masa cewa ina son sa? Idan ya mun dariya fa, zan iya jimrewa?

Ya kamata ki shirya kanki wa kowane amsa da zai iya baki. Kuma mai yiwuwa ki so yin wa wata amintaccen babba magana akan sa, kuma ki tuna, idan yayi miki dariya, kada ki bari ya canza ki, yarinya mai tabbaci!

Allah ya bada sa’a.

Nagode,
Babban Yaya.

Share your feedback