Abokiya ta na yanar gizo gizo na da matsala?

Ivie ta raba labarin ta mai buden ido

Na hadu da Anne a wani dakin yin tadi na yan mata a wani shafin sada zumunta. Tayi kamar da mai fara’a a hoton data sanya. Tana son yin ruwa kamar yadda nake so.

Anne ta san yadda zata saka ni jin farin ciki. Idan na gaya mata mahaifiyata ta mun fada, zata kawo wani labari mai ban dariya kuma zai saka ni dariya. Duk da yake bamu taba haduwa ba, na san cewa abokantakan mu nada kyau. Ta fahimce ni sosai.

Wani yamma, muna yin tadi kamar yadda muka saba. Ta tambaye ni nawa mahifiyata ta samu. Nace mata ban sani ba. A rana mai zuwa, ta tambaye ni ko mahaifiyata na ajiye kudi a gida ko banki. Na gaya mata wasu lokuta mahaifiyata na ajiye kudi a karkashin matashin ta. Tace naje na kawo mana wasu. Nayi mata bayani cewa bazan iya ba saboda bai kamata ba.

Anne ta daina amsa sakonni na. Nayi kewan ta kuma ina son na saka ta jin dadi. Ita ma zata iya mun haka. Sai na cire karamin canjin daga cikin matashin mahaifiyata. Sai na tura wa Anna sako na gaya mata abun dana yi. Ta amsa da wani hoto mai babban fuskan murmushi. Ta bukaci adireshi na. Na rubuta, na shirya zan tura.

Amma naji wani iri a cikin cikina. Irin wanda nake ji duk sanda nake jin tsoro. Na gaya wa Anna cewa ina ji kamar bai kamata na bata adireshi na ba. Ta tura muna wani hoton fuskan jin haushi. Tace zata nuna mun abun da take yin wa yan mata iri na. Nayi fahimta cewa ina cikin matsala. Naje wajan mahaifiyata na gaya mata abun dana yi. Naji kunyan abun dana yi.

Mahaifiyata ta gaya mun a koda yaushe na kawo rahoton kowane abokiya ta ba yanar gizo gizo mara hali mai kyau. Ta nuna mun yadda zan toshe Anne a dakin tadin. Ban san cewa yawancin shafin yanar gizo gizon zasu bar ni na toshe da kuma kai rahoton mutanen da ban so su tuntube ni ba. Sai kuma mahifiyata ta hana ni amfani da shafin yanar gizo gizon na wata uku. Sai ta saka ni na mata alkawari cewa ba zan sake yin sata ba kuma.

Yanzu na san cewa “Anne” bata taba kasance abokiya ta ba.

Yanar gizo gizo zai iya zama wajan nishadi amma ku tuna ku bi dashi kamar gidan ku. Baza ku bude kofa wa kowane bako ba. Ku kare kanku a wannan hanyar a yanar gizo gizo. Mu bude idon mu. Idan wani aboki ko wata abokiyar yanar gizo gizo suka saka mu jin wani iri, suka ce mu hadu dasu a waje, ko kuwa muyi kowane abu mara kyau kamar Anne, yakamta mu gaya wa wani baligin mutum da muka yarda da tun da wuri. Kada ku hadu da irin mutanen nan ko kuwa ku basu mallakin sirrin ku.

Yaya zamu tsirata kan mu a yanar gizo gizo? rarraba sidabbarun a nan kasa.

Share your feedback