Mercy ta rarraba labarin ta mai zurfi
Kawu Frank ya kasance babban aboki na. Idan yar uwata ta bata mun rai, ina kai rahoto wajan sa. Idan ina sha’awar wani yaro, ina asirta da kawu Frank. Zan iya gaya masa komai saboda ba zai taba hukunta ni ba. Yana ajiye mun sirri na kamar yadda nake ajiye nasa.
Amma a shekarar daya gabata, na lura cewa kawu Frank na duba mun kirji na. Na zata idanu na na mun karya ne. Sai na share zancen gaba daya.
Sai na lura cewa duk sanda yazo ziyara, baya son mu riga zama a dakin maziyarta kuma. A maimako, yafi son mu tsaya a waje muyi magana. Yana yin wasu irin maganganu akan jiki na. Na fara jin tsoro idan ina kusa dashi.
Wata rana, Kawu Frank yazo gida. Yar uwa ta na wajan aiki. Ina ta fargaba, amma ban nuna masa ba. Na zauna nesa dashi sai yace na matso kusa. Dana ki, sai ya matso kusa ya zauna a gefe na. Kafan na sani, ya fara tana mun cinya, na san cewa ba mafarki nake yi ba. Na tashi nace masa ya tafi.
Kawu na yayi mamaki. Fuskan sa ya canza! Koda yake, na gaya masa cewa abokantakar mu ya kare saboda ya karya yarda da nake masa. Ya kale ni da wani ido mara kyau, sai ya tafi.
Ina bakin ciki sosai. Ina son na kai rahoton sa, amma wa zan iya yin wa magana akan wanda na yarda da? Banda wannan, sanda wata yarinya a kungiyar matasar mu tace wani abokin iyalin su ya takura mata, mutane sun kira ta makaryaciya. Shiyasa nayi shiru.
Bayan nan, Kawu Frank ya daina zuwa gidan mu. Bayan lokaci kadan sai kuma ya fara zuwa. Wannan lokacin, sai ya shaku da yar uwata. Zai bata kananan abubuwa sai yace ta raba dani. Na ki karban dukka. Yar uwata ta kasa gane dalilin. Ta mun fada tace ina rashin kunya.
Amma na san cewa abun da Kawu Frank ke yi bai da kyau. Na san cewa idan ban yi magana ba, zai raunata yar uwata ma. Shiyasa na gaya mata komai.
Yar uwata tayi mamaki. Ta gaya wa Kawu Frank ya kyalle mu. Tace idan bai daina ba, zata kai rahoton sa zuwa iyayen mu kuma zasu kai rahoton sa a wajan yan sanda. Sai ta yabe ni dana zama jaruma. Nayi alfahari da kaina dana yi magana. Bazan sake jin tsoro kuma ba.
Idan wani da kuka yarda da yaci amanar ku zaku yi bakin ciki. Duke da haka, kada ku bari ayukan su ya hana ku yin magana. Koda yaushe ku tuna: Jikin ku mallakin ku ne. Ba wanda keda daman taba ku bada izinin ku ba. Ku kai rahoton a wajan wani ko wata amintaccen babba a koda yaushe, kada kuyi shiru.
Kun taba samun kanku a al’amarin Mercy? Ku rarraba labarin ku a nan kasa.
Share your feedback